Jerin kasashen da su ka fi Najeriya yawan jama’a a Duniya

Jerin kasashen da su ka fi Najeriya yawan jama’a a Duniya

A wannan makon nan ne mu ka tabbatar da cewa 'yan Najeriya sun doshi mutum miliyan 200 wanda hakan ya sa ta kara zama cikin kasashen da su ka fi kowane yawan mutane a Duniya. Najeriya yanzu ta sha gaban irin su Rasha, Bangladesh da sauran su.

Jerin kasashen da su ka fi Najeriya yawan jama’a a Duniya
Najeriya ta fi karfin irin su Rasha a wajen yawan jama’a

Ga dai Jerin kasashen da su ka fi Najeriya yawan al’umma nan mun kawo maku:

1. China

Duk Duniya babu kasa mai yawan jama’a irin Sin watau China. Alkaluman World Meters sun bayyana cewa akwai mutane kimanin Biliyan 1, 415, 000. 000 a kasar.

KU KARANTA: Wani Dattijo ya nemi Sojoji su ba shi gawar yaron sa

2. Indiya

Bayan Kasar ta Sin kuma sai Indiya a wajen yawan mutane. Yanzu haka Indiya akwai mutanen da su ka haura Biliyan 1, 350, 000, 000 kuma za su iya kerewa China.

3. USA

Kasa ta 3 da ta fi ko ina tarin al’umma a Duniya ita ce Amurka. Amurka ita ce ta farko a Nahiyar ta inda ake ta ke dauke da mutane da su ka haura Miliyan 320.

4. Indonesiya

Alkaluma sun nuna cewa Kasar Indonisiya mai mutum Miliyan 260 har-da-kari na bayan Amurka. Kasar ta Nahiyar Asiya na da albarkar mutane.

5. Brazil

Kasar Burazil da ke Yankin Amurka ita ce ta 5 a kaf Duniya kamar yadda alkaluma su ka tabbatar. Yanzu da mu ke magana akwai mutum Miliyan 210 a kasar.

6. Pakistan

Kasar da Najeriya ta ke bi wa wajen yawa ita ce Kasar Fakistan mai mutum Miliyan 200. Kusan ba makawa nan da wasu ‘yan shekaru kadan Najeriya za ta sha gaban Fakistan.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel