Wike, Ortom Da Makinde Ba Zasu Sauya Sheka Zuwa APC Ba, PDP
- Wasu rahotanni sun nuna cewa akwai alamun tsagin gwamna Nyesom Wike na Ribas zasu mara wa Bola Tinubu baya a 2023
- Kwamitin PCC-PDP ya karyata rahoton, Sanata Dino Melaye ya yi ikirarin cewa har yanzun ana tattaunawa don neman sulhu
- Makusancin gwamna Samuel Ortom, ɗaya daga mambobin G5 yace komai ka iya faruwa gabanin 2023
Sabanin jita-jitar da ake yaɗawa cewa Gwamna Wike ya yanke shawarin mara wa Bola Tinubu na jam'iyyar APC baya, makusantan Atiku Abubakar a PDP sun ƙaryata rahoton.
Nyesom Wike, jagoran tawagar G5 da ta kunshi gwamnonin PDP 5 da wasu jiga-jigai, sun ce tallata takarar Atiku zata yuwu ne kaɗai idan shugaban PDP na ƙasa, Iyorchia Ayu, ya yi murabus.
Gwamnan Ribas tare da takwarorinsa na jihohin Abiya, Benuwai, Enugu da Oyo sun tsaya kai da fata dole Ayu ya sauka bisa hujjar cewa bai kamata ɗan takarar shugaban kasa da shugaban PDP su fito daga yanki ɗaya.
A watan Satumba, gwamnonin da wasu kusoshi kamar tsoffin gwamnoni, Donald Duke (Kuros Riba), Jonah Jang (Filato), da Olusegun Mimiko (Ondo) da wasu jiga-jigai suka janye daga kwamitin kamfen Atiku.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Jaridar Punch ta tattaro cewa tsohon mataimakin shugaban ƙasan ya zaɓi tsaya wa daga gefe, inda ya jaddada cewa Ayu ne kaɗai zai yanke zai sauka ko kuma zai zauna a kujerarsa.
Bisa haka ne aka fara yaɗa jita-jitar cewa sakamakon gazawar Atiku na tunɓuke Ayu, Wike ya cimma matsayar marawa Tinubu baya, ya hasaso cewa ya fi Peter Obi damar lashe zabe.
Wata majiya mai alaƙa da batun ta shaida wa wakilin Punch cewa Wike ba zai bar PDP ba, amma zai tattara wa Bola Tinubu kuri'u a jihar Ribas.
Menene gaskiyar wannan jita-jitar?
Amma da yake zantawa da wakilin jaridar kan haka, kakakin kwamitin zaɓe na tawagar kamfen Atiku (PCC-PDP), Dino Melaye, ya yi fatali da raɗe-raɗin Wike na shirin sauya sheka.
Sanatan ya jaddada cewa ana ci gaban da zaman tatttaunawa a tsakanin tsagin guda biyu domin kawo karshen rikicin cikin gida.
"Muna ci gaba da zaman neman sulhu kuma shi (Wike) ba zai bar jam'iyya ba," inji Sanata Melaye.
Haka nan daraktan kwamitin sadarwa na PCC-PDP, Chief Dele Momodu, yace zai tsoma baki kan wannan batu ne kaɗai idan Wike ya yanke matsayar inda ya dosa.
"Ba zan ce komai ba har sai ya bayyana matsaya," inji shi kuma ya ƙara da cewa bai san komai ba kan rahoton tsagin Wike sun kulla ƙawance da ɗan takarar shugaban ƙasa na APC.
Hadimin Atiku kuma daraktan kamfen Atiku/Okowa gida-gida a Borno, Mustapha Shehu, yace tuni tawagar yakin neman zaɓe ta matsa gaba, yace, "Gwamnan Ribas bai kai matsayin da yake tunani ba."
"Sakon ya isa kowane layi, Atiku ne ya dace da 'yan Najeriya shi suke so. Shiyasa muka yanke ci gaba da harkokin mu ba tare da G5 ba, duk da kofofin Atiku a buɗe suke a zauna sulhu."
Haka nan wani Makusancin Gwamna Ortom na kusa, wanda ya bukaci a boye bayanasa, yace da yuwuwar gwamna Wike ya haɗa inuwa da tsohon gwamnan Legas.
Atiku Zai Gana da Gwamnan Wata Jam'iyya da Sarakuna, PDP Ta Fara Kullin Shawo Kan Su Wike
A wani labarin kuma jirgin ɗan takarar shugaban kasa na PDP zai dira jihar Anambra ranar Alhamis, ya shirya zama gwamna Soludo
A wata sanarwa da Darakta Janar da kwamitin kamfen Atiku /Okowa, Obiora Okonkwo ya fitar, yace Atiku zan gudanar da muhimman taruka a ziyarar da zai kai Anambra.
Bugu da ƙari, yace PDP ta sake kafa tawaga ta musamman da zata ƙara jaraba yunkurin rarrashin tsagin gwamna Wike da ake kira G5.
Asali: Legit.ng