El-Rufai: Abubuwa 2 da ya Zama Wajibi Magajin Buhari Ya Yi Yaki da Su a Mulki

El-Rufai: Abubuwa 2 da ya Zama Wajibi Magajin Buhari Ya Yi Yaki da Su a Mulki

  • Malam Nasir El-Rufai ya na ganin babu makawa, sai an yi watsi da tsarin biyan tallafin man fetur
  • Gwamnan na jihar Kaduna ya ba shugaban kasan da zai karbi mulki a 2023 ya cire tallafi a Najeriya
  • Tsohon Ministan ya kuma bada shawarar a dauki matakin da zai hana tashin kudin kasashen waje

Kaduna - Gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai ya hada wanda zai zama sabon shugaban Najeriya da aiki, ya fadi abubuwan da su ke jiransa a ofis.

Leadership a wani rahoto, ta ce Malam Nasir El-Rufai ya ce dole ne wanda zai karbi mulkin kasar nan ya yi kokarin shawo kan matsalar tattalin arziki.

Gwamna Nasir El-Rufai ya ce don haka akwai bukatar a magance matsalar tallafin man fetur da kuma tashin da kudin kasar waje suke yi a halin yanzu.

Kara karanta wannan

2023: An Sanar da Ranar Da Za A Fada Wa Kiristocin Kudancin Kaduna Dan Takarar Gwamna Da Za Su Zaba

Amma kuma Gwamnan na Kaduna ya ce idan shugaban kasar da aka zaba ya yi wadannan abubuwa, zai yi masa wahala ya zarce kan mulki a 2027.

Bankin Duniya ya yi taro a Najeriya

El-Rufai ya yi wannan jawabi a wajen wata tattaunawa da bankin Duniya ya shirya a garin Abuja a kan abin da ya shafi cigaban tattalin arzikin Najeriya.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Da aka yi masa tambaya a kan cire tallafin man fetur, jaridar ta rahoto tsohon Ministan birnin Abuja yana cewa dole a kawo karshen tsarin nan.

El-Rufai
Gwamna El-Rufai wajen taron APC Hoto: @GovKaduna
Asali: Twitter

An yi niyyar cire tallafin man fetur a bana

A cewar Gwamnan, a baya Gwamnatin Muhammadu Buhari ta yarda za a janye tallafin a shekar nan, amma aka fasa sai zuwa tsakiyar shekarar 2023.

Kamar yadda El-Rufai ya fada a taron, Gwamnatocin jihohi da ‘yan kasuwa sun yarda cewa babu yadda aka iya, wajibi ne a hakura a daina biyan tallafin mai.

Kara karanta wannan

An Samu Wadanda Za Su Kai Bankin CBN Kotu a Kan Tsarin Cire N20, 000 a Rana

Idan ta kama, shugaban kasar da zai zo ya yi wa’adi daya a mulki, El-Rufai yana ganin babu matsala, muddin gwamnati ta huta da kashe makudan kudi.

A jawabin, tsohon Ministan kasar ya ce yana alfahari da aikin da ya yi a gwamnatin Obasanjo, ya ce sun dauki wasu matakan da suka kai ga samun cigaba.

Da za a cire tsoro a dauki matakan da suka dace, Gwamnan ya ce Najeriya za ta cigaba sosai.

Rikicin APC a jihar Bauchi

An ji labari tsohon Gwamnan Bauchi, bai tare da ‘Dan takaran jam’iyyar APC, AVM Sidique Abubakar (rtd), yana goyon bayan wanda ya hana shi tazarce.

An ji Mohammed A. Abubakar yana mai cewa: “Ina rokon Allah ya cigaba da yi masa (Gwamna Bala Mohammed) jagoranci wajen tafiyar da harkar jihar nan.”

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng