'Yan Bindiga Sun Harbi Daraktan Matasa Na Kwamitin Kamfen Atiku a Jihar Ribas

'Yan Bindiga Sun Harbi Daraktan Matasa Na Kwamitin Kamfen Atiku a Jihar Ribas

  • Wasu mutane ɗauke da bindigu da ake zaton yan daban siyasa ne sun harbi Daraktan haɗa kan matasa da PDP-PCC a jihar Ribas
  • Lamarin na ranar Laraba da daddare ya faru ne wata ɗaya kenan bayan an sace Mista Rhino Owhorkire, an tilasta masa barranta da Atiku
  • Hukumar 'yan sandan jihar ta tabbatar da aukuwar lamarinn tace tuni ta fara bincike

Rivers - Wasu 'Yan bindiga da ake zargin yan daban siyasa ne sun harbi Daraktan tattara matasa na kwamitin yakin neman zaɓen Atiku/Okowa a jihar Ribas, Rhino Owhorkire.

Jaridar Punch ta tattaro cewa tsagerun sun harbi Owhorkire ne yayin da yake hanyar komawa gida a garin Aluu, karamar hukumar Ikwerre ta jihar ranar Laraba da daddare.

Taswirar jigar Ribas.
'Yan Bindiga Sun Harbi Daraktan Matasa Na Kwamitin Kamfen Atiku a Jihar Ribas Hoto: punchng
Asali: UGC

Wannan na zuwa ne wata ɗaya tal bayan an yi garkuwa da Daraktan matasan kuma aka tilasta masa ya furta cewa ya janye goyon bayansa ga Atiku Abubakar.

Kara karanta wannan

2023: "Ka Ci Zaɓe Ka Ci Zabe" Yadda Dubun Dubatar Magoya Baya Suka Yi Maraba da Tinubu a Jihar Arewa

A farkon watan Nuwamba, an ga Owhorkire a cikin wani Bidiyo yana furta kalaman barranta daga goyon bayan Atiku, a wani wuri mai kama da Kogo.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

A cikin Bidiyon an ga Daraktan matasan kewaye da wasu mutane, waɗanda suke dakon jin abinda zai fito daga bakinsa duk da fuskarsa ta nuna ƙarara ya firgita.

Yadda aka harbi daraktan matasan jiya da dare

Da yake labarta yadda farmakin ya faru da safiyar Alhamis, wata majiya tace maharan sun fara da fasa tayoyin motar Owhorkire daga bisani suka bude masa wuta da gilashi.

Mutumin wanda ya nemi a sakaya sunansa saboda tsoron abinda zai je ya dawo yace Mista Owhorkire na cikin yanayi kuma yanzu haka yana kwance a wani Asibiti da ba'a bayyana ba.

A cewarsa, "Shi haifaffen garin Aluu ne, yana cikin tafiya zai koma gida jiya da daddare wasu mutane da ba'a gane su ba suka harbe shi. Sun fasa tayoyinsa da harsashi sannan suka buɗe nasa wuta ta Gilashin mota."

Kara karanta wannan

2023: Na Gode Allah da Tinubu Bai Zabe Ni a Matsayin Abokin Takara Ba, Tsohon shugaban Majalisa

"Sakamakon haka ya samu raunuka a bakinsa, sun farfasa masa baki. Yanzu da nake magana da ku yana cikin mawuyacin hali, sun yi raga-raga da bakinsa, yana kwance a Asibiti da ba'a faɗa ba."

Wane mataki hukumomin tsaro suka dauka?

Yayin da aka tuntuɓi jami'ar hulɗa da jama'a ta rundunar 'yan sandan jihar Ribas, Grace Iringe-Koko, ta tabbatar da lamarin, tace tuni dakaru suka tsunduma bincike.

"Eh ya faru, na yi magana da DPO na yankin kuma yanzun muna kokarin tattara bayanai, amma ina tabbatar muku mun fara bincike. Zamu tabbatar masu hannu sun fuskanci hukunci."

A wani labarin kuma PDP Ta Ɗau Zafi, Wike Da Ortom Sun Yi Watsi da Atiku Yayin da Suka Ci Karo a Filin Jirgi

Rigimar da ke tsakanin dan takarar shugaban kasa na PDP, Atiku Abubakar da fusatattun gwamnonin jam'iyyar da ake kira G5 ta kara ya fitowa fili a ranar Litinin.

Kara karanta wannan

2023: Atiku Ya Kai Kamfen Dinsa Filato, Ya Yi Alkawarin Dawo Da Zaman Lafiya Da Farfado Da Tattalin Arziki

Gwamna Ribas, Nyesom Wike, da takwaransa Ortom na jigar Benuwai sun yi watsi da Atiku a filin jirgin Makurɗi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262