Zaben 2023: 'Yan Arewa Za Su Ba Tinubu Kuri'u Sama Sa Miliyan 12, Jigon Arewa Ya Fadi Ta Yaya
- Wani jigon APC, Danladi Bako, ya bugi kirjin cewa yan arewa za su ba Asiwaju Bola Tinubu kuri'u miliyan 12 a zaben 2023
- Bako ya jaddada cewa har yanzu shugaban kasa Muhammadu Buhari na nan da farin jininsa kuma zai yi tasiri sosai wajen nasarar da APC zata samu
- Tsohon kwamishinan na jihar Sokoto ya ce Tinubu zai samu fiye da kaso 25 na kuri'un yan Najeriya
Daraktan dabarun sadarwa na kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa na jam'iyyar All Progressives Congress (APC), Danladi Bako, ya bayyana yadda za su samu kuri'unsu a zaben 2023.
Bako ya ce da taimakon shugaban kasa Muhammadu Buhari, gwamnoni da sauransu, Asiwaju Bola Tinubu zai samu kuri'u miliyan 12 daga yankin arewacin Najeriya, PM News ta rahoto.
Tinubu zai samu kuri'un yan Najeriya fiye da kaso 25
Fitaccen dan kasuwan ya ce dandazon jama'ar da suka yi tururuwa a wajen kaddamar da manufofin APC a Jos, jihar Filato kwanan nan ya nuna cewa har yanzu shugaban kasar na nan da farin jininsa.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Bako wanda ya kasance tsohon kwamishina a jihar Sokoto ya ce Tinubu zai samu fiye da kaso 25 cikin 100 na jihohi 36 da babban birnin tarayya, rahoton Vanguard.
Ya ce:
"A iya sanina da zaben 2023, arewa za ta kawowa APC kuri'u miliyan 12.
"Na yarda cewa babu wani babban dan takara daga arewa da zai iya kawo irin kuri'un da Buhari ya saba kawowa.
"Babu matala kan wannan domin gwamnonin arewa maso yamma sun lashe zabe sau biyu kuma za su tabbatar da nasarar APC.
"Shugaban kasar na da farin jini sosai kuma ra'ayinsa na da matukar muhimmanci a zaben, yayin da sauran yan takarar basu fito daga yankin ba.
"Saboda haka. dan takarar shugaban kasa na APC zai tara kuri'u masu yawa don lashe arewa maso yamma da Najeriya baki daya."
Ya kara da cewar kasancewar Sanata Aliyu Magatakarda shugaban jam'iyyar a jihar Sokoto zai yi tasiri ga APC sosai a jihar.
"Koda dai Wamakko ba gwamnan jihar bane a yanzu har yau yana da tarin magoya baya domin ya ci gaba da bayar da fifiko wajen jin dadin mutane a jihar."
Nagode Allah da ban zama abokin takarar Bola Tinubu ba, Dogara
A wani labarin, tsohon kakakin majalisar wakilai, Yakubu Dogara ya bayyana cewa yana tsananin godiya ga Allah da bashi Bola Tinubu ya zaba domin zama abokin takararsa a zaben 2023 ba.
Dogara ya bayyana masu tallata tikitin Musulmi da Musulmi a matsayin mahaukata kuma mutane masu hatsari.
Asali: Legit.ng