Ban Fadi Kalmomin Dana Fada Na Zagi Da Wata Manufa Ba Sai Dan Motsa Jama'a

Ban Fadi Kalmomin Dana Fada Na Zagi Da Wata Manufa Ba Sai Dan Motsa Jama'a

  • A wani faifen bidiyo da bai wuce dakika talatin ba aka jiyo shugaban masu rinjaye na majalissar na cewa " ko ka zabi APC, ko kaci ubanka"
  • Sai dai dan majalissa ya musanta zargin cewa yana nufin yin amfani da karfin tuwo wajen cin zabe, yace yayi ne kawai da zimmar a motsa jam'iyya
  • Tuni dai yan jam'iyyar adawa daga bangarori da dama na siyasa ke ganin kalaman shugaban majalissar bai dace ba.

Abuja: Shugaban masu rinjaye na majalisar wakilai kuma jigo a jam’iyyar All Progressives Congress (APC), Ado Doguwa, ya fadi wani kalami da ya janyo ce-ce-ku-ce a baya-bayan nan da ya yi a wani faifan bidiyo da ya yadu a kafar intanet wanda legit.ng hausa ta samu.

A kalaman nasa wanda ya furta a gaban magoya bayansa yana mai cewa:

Kara karanta wannan

Daga hannun PDP muka gaji matsalar Boko Haram : FG Ta Maidawa Atiku martani

"Wallahi ko ka zabi jam'iyyar APC, ko kuma kaci Ubanka."

Sai dai kuma shugaban masu rinjaye na Majalisar ya yi karin haske kan kalaman nasa a yayin wani shiri na tsaye a gidan Talabijin na Channels TV, inda ya ce manufarsa ita ce zaburar da magoya bayansa, ba tsoratar da su ba.

Alhassan Doguwa
Ba Fadi Kalmomin Dana Fada Na Zagi Da Wata Manufa Ba Sai Dan Motsa Jama'a Hoto: Premium Times
Asali: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Doguwa yace:

“Wannan ba barazana ba ce. Ba zan taba yi wa masu zabe barazana ba. Abin da ba ku sani ba game da jihar Kano (shine) jihar Kano fage ce ta siyasa. kuma muna da ilimin mu na musamman wanda ya shafi wasu kalmomin siyasa da muke amfani da su".
"A jihar Kano dole ne kayi aiki da wasu hanyoyi ko kalmomi wanda zasu sa jama'a wato magoya baya su motsa"

Kara karanta wannan

Emefiele Yana Amfani Da Matsayinsa Don 'Azabtar' Da Yan Siyasa, Gwamnan Arewa Mai Karfin Fada Aji Ya Yi Zargi

Da yake amsa tambaya kan yadda kalaman nasa suka janyo cece-cece kuce da kuma barazana, Doguwa yace wannan batun dama sun saba.

Ita siyasar Kano wata siyace mai daure kai da kuma shiga duhu, shi yasa akwai abubuwa da mutum zai aikita a zahiri zaka ga kamar yana nufin barazana ne, amma ba barazana bane, kamar yadda nima na fada, ba barzana nake yiwa mutane ba inji doguwa.

Shugaban Jam'iyyar APC Na Jihar Kano Yace Koda Tsiya-Tsiya Sai Sun ci Zabe A jihar

Shugaban jam'iyyar APC na jihar Kano Abdullahi Abbas yace koda tsiya-tsiya sai sunci zaben gwamnann jihar kano.

Shugaban na wannna n kalamin ne lokacin da jam'iyyar APC ta jihar kano ta bude yakin neman zabenta na jihar a karamar hukumar Gaya, wadda daya ce kuma daga cikin masarautin kano.

Asali: Legit.ng

Authors:
AbdulRahman Rashida avatar

AbdulRahman Rashida