2023: Zan Ba Matasa Da Mata Aikin Yi, Atiku Ga Al’ummar Nasarawa

2023: Zan Ba Matasa Da Mata Aikin Yi, Atiku Ga Al’ummar Nasarawa

  • Atiku Abubakar ya sake daukar alkawarin kula da matasa da mata idan aka zabe shi a matsayin magajin Buhari
  • Dan takarar shugaban kasa na PDP ya sha nanata bukatar baiwa mata da matasa aiki a kasar nan
  • Da yake jawabi a gangamin yakin neman zabensa a Lafia, Atiku ya sake daukar alwashin magance matsalolin matasa da mata

Nasarawa - Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar Peoples Democratic Party, PDP, Alhaji Atiku Abubakar, ya bukaci mutanen jihar Nasarawa da su zabi jam'iyyarsa a zaben 2023, yana mai shan alwashin habaka ababen more rayuwa a jihar idan aka zabe shi.

Tsohon mataimakin shugaban kasar ya bayyana hakan ne a gangamin yakin neman zabensa a Lafia, babban birnin jihar Nasarawa, jaridar The Cable ta rahoto.

Atiku Abubakar
2023: Zan Ba Matasa Da Mata Aikin Yi, Atiku Ga Al’ummar Nasarawa Hoto: @atiku
Asali: Twitter

Ya ce:

"Ina mai mika godiya ga mutanen Nasarawa kan wannan goyon bayan. Ina mai jaddada jajircewarmu na daukar matasa da mata aiki a Najeriya. Wannan ne dalilin da yasa gwamnatina ta ware dala biliyan 10 saboda haka. Za mu daukaka ababen more rayuwa a Nasarawa idan aka zabe ni."

Kara karanta wannan

Kowa ya huta: Atiku ya fadi yadda zai yi kungiyar ASUU idan ya gaji Buhari a zaben 2023

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A nashi bangaren, shugaban PDP na kasa, Sanata Iyorcha Ayu ya yi hasashen cewa Atiku zai lashe yankin arewa ta tsakiya a zabe mai zuwa, rahoton Vanguard.

Shugaban jam'iyyar ya bukaci wadanda suka bar jam'iyyar da su dawo don shiga jirgin nasara domin jam'iyyar ce za ta lashe zabe mai zuwa.

Ya ce:

"Atiku zai samu mafi yawan kuri'unsa daga arewa ta tsakiya. Ina sanya ran Nasarawa za ta ba Atiku kaso 90 da kuri'u. Mun fara wannan tafiyar a Nasarawa a 1998. Ina mai umurtan wadanda suka bar jam'iyyar da su dawo jam'iyya mai nasara, ku zo ku bi jirgin nasara."

Ayu ya bukaci magoya baya a Nasarawa da su zabi yan takarar PDP daga sama har kasa a jihar.

Atiku ya bukaci Tinubu ya fito ya yi bayanin dukiyarsa

Kara karanta wannan

Atiku Ya Bayyana Abubuwan da Zai Tunkara a Ranar da Ya Fara Shiga Fadar Aso Rock

A wani labarin, dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar ya bukaci babban abokin hamayyarsa, Bola Tinubu ya zo ya yi bayani a kan dukiyarsa.

Atiku ya dasa ayar tambaya kan kadarorin da Tinubu ya ce ya gada domin a cewarsa babu yadda za a yi wanda ya yi ikirarin fitowa daga gidan talakawa ya gaji kadarori.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng