Babu Wanda Zai Iya Raba Kan Gwamnonin G-5 Masu Adawa da Atiku, in Ji Bode George

Babu Wanda Zai Iya Raba Kan Gwamnonin G-5 Masu Adawa da Atiku, in Ji Bode George

  • Tsohon mataimakin shugaban jam’iyyar PDP na kasa ya bayyana kadan daga halayen gwamnonin da ke ba Atiku ciwon kai gabanin zaben 2023
  • Bode George ya ce sam babu wata matsala ko yarjejeniya da za ta sa gwamnonon G-5 su jefar da adawa da dan takarar shugaban kasa na PDP
  • Atiku Abubakar na ci gaba da fuskantar barazana daga wasu gwamnonin jam’iyyar PDP biyar masu adawa da shugabancin PDP

Najeriya - Tsohon mataimakin shugaban jam’iyyar PDP na kasa, Olabode George ya ce, gwamnonin G-5 masu adawa da Atiku suna nan kyam kan adawarsu, kuma babu abin da zai iya raba kansu.

Bode George ya bayyana hakan ne tare da cewa, gwamonin biyar sun kulla amintarsu ne bisa daidaito, adalci da gaskiya, The Nation ta ruwaito.

Ya yi wannan magana ne a martaninsa ga ganawar gwamna Aminu Tambuwal na jihar Sokoto da daya daga cikin gwamnonin biyar na G-5.

Kara karanta wannan

Kano: Mutanen Ganduje Zasu Jagoranci Tawagar Yakin Neman Zaben Gwamna a Jam'iyyar Kwankwaso

Bode George ya caccaki Atiku
Babu Wanda Zai Iya Raba Kan Gwamnonin G-5 Masu Adawa da Atiku, in Ji Bode George | Hoto: thenationonlineng.net
Asali: UGC

Yadda rikicin cikin gida na PDP ke gudana

Idan baku manta ba, Tambuwal ya shaidawa manema labarai a ranar Lahadi cewa, manufar ziyararsa ta jihar Benue ba komai bane face tattauna mafita ga dumamar yanayin PDP a kasar nan tare da gwamna Samuel Ortom.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sauran gwamnonin G-5 sun hada da gwamna Nyesom Wike na jihar Ribas, Ifeanyi Ugwuanyi na jihar Enugu, Seyi Makinde na jihar Oyo da Okezie Ikpeazu na jihar Abia.

Babu abin da zai iya raba kan G-5

Da yake martani ga lamarin, Bode George ya ce ziyarar da Tambuwal ya kai wa Ortom ba za ta yi wani tasiri ba, domin kuwa hakan ba zai raba kan gwamnonin biyar ba, wanda Ortom na cikinsu.

Ya bayyana cewa, ya yiwa Ortom farin sani, kuma a iya fahimtarsa mutum ne mai riko da kalamansi, don haka ba zai amince da rusa G-5 ba, ya shaidawa The Nation.

Kara karanta wannan

Rikicin PDP: Sau 5 Ina Zama da Gwamna Wike, Atiku Abubakar Ya Fallasa Inda Matsalar Take

George ya kuma bayyana kaduwa da mamakin cewa, ta yaya Atiku da ya gaza hada kan jam’iyyar PDP zai iya shawo kan matsalolin da kasar nan ke ciki.

A tun farko, gwamnonin biyar sun kafa kungiyar ne tare da bayyana matsayarsu cewa, ba za su yi dan takarar shugaban kasa na PDP, Atiku Abubakar kamfen ba a zaben 2023.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.