Sau Biyar Ina Zama da Gwamna Wike Don Kawo Karshen Rikicin PDP, Atiku Ya Magantu

Sau Biyar Ina Zama da Gwamna Wike Don Kawo Karshen Rikicin PDP, Atiku Ya Magantu

  • Atiku Abubakar, ɗan takarar shugaban kasa a PDP yace ya gana da gwamna Wike akalla sau 5 don shawo kan rikicin PDP
  • Tsohon mataimakin shugaban kasan tare da abokin gaminsa sun halarci tattaunawar da aka shirya wa yan takara
  • PDP ta tsinci kanta cikin rigima ne tun bayan zaɓen fidda gwani da kuma ayyana Okowa a matsayin abokin takarar Atiku

Mai neman zama shugaban kasa a inuwar PDP, Alhaji Atiku Abubakar, yace ya zauna da gwamna Nyesom Wike na jihar Ribas domin kawo karshen rikicin cikin gida amma abu ya ki cinye wa.

Tsohon mataimakin shugaban kasan ya faɗi haka a wurin taron da ake shirya wa yan takara, wanda Channels TV da wasu ƙawayenta suka ɗauki nauyi ranar Lahadi.

Atiku Abubakar.
Sau Biyar Ina Zama da Gwamna Wike Don Kawo Karshen Rikicin PDP, Atiku Ya Magantu Hoto: channelstv
Asali: UGC

Yayin da aka tambaye shi meyasa har yanzun suka gaza kawo karshen dambarwan cikin PDP tsawon watanni, Atiku ya ce:

Kara karanta wannan

Kowa ya huta: Atiku ya fadi yadda zai yi kungiyar ASUU idan ya gaji Buhari a zaben 2023

"Na zauna da gwamna Wike sau biyu a Patakwal, mun kuma gana sau biyu a birnin tarayya Abuja, haka nan ni da shi mun gana a Landan."

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"A halin yanzun tsaikon ba daga ɓangare na bane, daga ɗayan tsagin ne. Ina nan ina dakon shi," inji shi ba tare da ya bayyana yadda tattaunawarsu ta kasance ba.

Atiku Abubakar ya halarci shirin tare da abokin takararsa kuma gwamnan jihar Delta, Ifeanyi Okowa.

Asalin rikicin jam'iyyar PDP

Gwamna Wike ya gamu da cikas wanda ya kawo ƙarshen burinsa na zama shugaban kasa a 2023 lokacin da Atiku ya ɗaɗa shi da ƙasa a zaben fidda gwanin PDP a watan Mayu.

Bayan haka, Atiku, tsohon mataimakin shugaban kasa ya kara kulad da Wike bayan ya tsallake shi ya ɗauki gwamna Okowa a matsayin abokin takararsa.

Kara karanta wannan

Gwamna Wike Ya Fara Ƙalaman Nuna Wanda Zai Mara Wa Baya Tsakanin Atiku da Tinubu a 2023

Tun daga nan gwamna Wike ya fara takun saƙa da Atiku Abubakar kan shugabancin Iyorchia Ayu. Shi da sauran gwamnonin G5 sun matsa lamaba sai shugaban PDP na ƙasa ya yi murabus.

Tsagin Wike sun kafe kai da fata cewa dole Ayu ya sauka ya ba ɗan kudu matukar PDP na zon su dawo a tafi tare da su.

A wani labarin kuma Daraktan Yakin Neman Zaben Atiku Ya Gana da Gwamnan Tsagin Wike Watau G5

Gwamna Aminu Tambuwal na jihar Sakkwato ya ziyarci takwaransa na jihar Benuwai, Samuel Ortom kan rigingimun da suka hana PDP zaman lafiya.

Tambuwal yace rikicin PDP ba yaƙi bane, sabanin ra'ayin siyasa ne kuma ba zasu huta ba har sai sun warware komai jam'uyyar PDP ta dunƙuƙe wuri ɗaya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262