Rigimar PDP: Tambuwal Ya Ziyarci Gwamna Ortom, Yace Abun da Yaki Bane
- Gwamna Aminu Tambuwal ya ziyarci takwaransa na jihar Benuwai, Samuel Ortom kan rigingimun da suka addabi PDP
- Daraktan Kamfen PDP na kasa yace rikicin da ake gani a jam'iyyar ba yaki bane, sabanin siyasa ne da zasu shawo kai nan kusa
- Gwamna Ortom ya jaddada cewa shugabancin jam'iyyar PDP ne ya haddasa duk halin da ake ciki a yanzu
Benue - Gwamnan jihar Sakkwato, Aminu Waziri Tambuwal, yace rigingimun da suka addabi PDP ba yakin neman suna bane, saɓani ne na siyasa da za'a warware nan gaba kaɗan.
Tambuwal, darakta janar na yakin neman zaɓen PDP, ya bayyana haka ne ranar Lahadi yayin da ya ziyarci takwaransa na jihar Benuwai, Samuel Ortom a Makurdi.
Ya ce ya kawo wannan ziyara ne kan rigingimun da suka shafi PDP kana ya tafa wa rawar da gwamna Ortom ke takawa a PDP a fannoni daban-daban.
Vanguard ta rahoto Tambuwal na cewa:
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
"Mun samu lokacin tattaunawa kan abubuwan dake faruwa a jam'iyyar mu. Gwamna Ortom jagora ne a PDP idan kuka duba tarihinsa da matsayin da ya taka a yanzu."
"Ƴa rike muƙamai masu muhimmanci a harkokin tafiyar da jam'iyya, na faɗa a baya kusan watanni uku da suka shuɗe, rikicin dake faruwa a cikin gida ba sabo bane kuma ba yaki bane illa saɓanin siyasa."
"Ko a cikin iyalan mu muna samun saɓani, wani lokacin mu yi matsaya ɗaya, idan irin haka ta faru da zaran mun ɗinke ɓaraka zaka ga mun kara karfi fiye da baya. Saboda haka muna kan aiki, mun zauna lokuta da dama."
Tun da farko gwamnan Samuel Ortom yace sun tattauna batutuwa da dama ciki har da rabuwar PDP da G5, tsagin da yake mamba bisa jagorancin gwamna Wike.
Dalilin da Ya Sa Nake Goyon Bayan Tinubu Duk Ba Jam'iyyar Mu Ɗaya Ba, Sanatan PDP Ya Faɗi Abinda Ya Hango
Ortom yace:
"Mun tattauna batutuwa harda darewar PDP da G5 da nake mamba, ya zo ne don ganin yadda zamu haɗa kai mu yi aiki tare kuma na ce masa kofa ta buɗe take, mu duka 'ya'yan PDP ne."
"Amma na faɗa cewa shugabancin jam'iyya ya gaza amfani da wannan kalubalen wajen ƙara karfi tun daga babban taron mu, an gaza lalubo hanyar masalaha sai amfani da rigingimu ta wata fuskar daban."
Abinda Jam'iyyar APC Zata Yi Ta Lashe Babban Zabe Mai Zuwa, Buhari
A wani labarin kuma Shugaban Ƙasa, Muhammadu Buhari, ya nemi shugabannin APC su haɗa kai su tabbatar jam'iyyar ta samu galaba a 2023
Buhari ya bayyana haka yayin da ya karɓi bakuncin ɗan takarar gwamnan Katsaina a APC, Dikko Radda, da abokin takararsa, Farouk Jobe a gidansa na Daura.
Shugaban ƙasan yace matukar jam'iyyar APC ta haɗa kai a cikin gida zata iya kai labari, ya jaddada kudirinsa na ganin an gudanar da sahihin zaɓe a 2023.
Asali: Legit.ng