Atiku Ya Sake Zakulo Wani Gwamna Mai Ci, Ya Naɗa Shi Muhimmin Mukami a Kwamitin Kamfe
- Bayan rantsar da sabon gwamnan jihar Osun, Atiku Abubakar ya naɗa shi mukami a kwamitin yakin neman zaben PDP
- Darakta Janar na PDP-PCO, Gwamna Aminu Tambuwal ne ya sanar da haka, yace naɗin zai fara aiki nan take
- Atiku Abubakar, ɗan takarar shugaban ƙasa a jam'iyyar PDP na fatan doke Tinubu na jam'iyya mai mulki a zaɓe mai zuwa
Abuja - Kwamitin yakin neman zaben shugaban ƙasa na jam'iyyar PDP ya amince da naɗa gwamnan Osun, Ademola Adeleke, a matsayin mamba tawagar kamfe.
Jaridar Punch ta tattaro cewa kwamitin ya naɗa gwamna Adeleke a matsayin shugaban kwamitin daidaito na shiyyar kudu maso yammacin Najeriya.
Wannan na kunshe ne a wata sanarwa mai ɗauke da sa hannun Darakta Janar na PDP-PCO, gwamna Aminu Waziri Tambuwal na jihar Sakkwato.
Haka zalika sanarwar ta sanar da naɗin wasu ƙusoshin mambobin jam'iyyar PDP a muƙamai daban-daban na kwamitin domin ƙara karfin jan ragamar kai Atiku Abubakar fadar shugaban kasa.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Legit.ng Hausa ta fahimci cewa an naɗa Sanata Dino Melaye a matsayin daraktan harkokin watsa labarai.
"Baki ɗaya waɗan nan naɗe-naɗe zasu fara aiki ne nan take," inji gwamna Aminu Tambuwal.
Jerin yadda jadawalin naɗin ya kasance
Kwamitin daidaito na shiyyoyin Najeriya ya ƙunshi:
1. Kudu maso gabashin Najeriya: Sanata Theodore Orji a matsayin shugaban kwamiti.
2. Kudu maso kudu: gwamnan jihar Bayelsa, Sanata Duoye Diri, (shugaban kwamiti).
3. Kudu maso yamma: Sanata Ademola Adeleke, gwamnan jihar Osun a matsayin shugaba.
4. Arewa ta tsakiya: Sanata Gabriel Suswam (shugaba).
5. Arewa maso gabashin Najeriya: Gwamnan Taraba, Darius Ishiaku a matsayin shugaba.
6. Arewa maso yamma: Adamu Aleiru ne zai jagorancin kwamitin.
Bugu da ƙari, kwamitin yakin PDP ya kuma yi sabbin naɗe-nafe a sashin ofisoshin sadarwa na shiyya-shiyya.
A wani labarin kuma Tsohuwar Minista a Mulkin PDP Ta Jingine Atiku, Ta Bayyana Zabinta a 2023
Tsohuwar ministar ilimi a Najeriya daga shekarar 2006 zuwa 2007, Obiageli Ezekwesili, tace a iya sanin da ta yi wa kowa, ta sanya manyan 'yan takara uku a Sikeli.
A cewar tsohuwar ministar kuma tsohuwar mataimakiyar shugaban bankin duniya, ba yadda za'a yi tana ganin Peter Obi ta zarce ta zabi wani daban a cikinsu.
Asali: Legit.ng