Tsohon Mataimakin Gwamna da Wasu Jiga-Jigan PDP Sun Koma APC a Jihar Gombe
- Shugaban matasan PDP na shiyyar arewa maso gabas, Kabiru Jauro da tsohon mataimakin gwamna sun koma APC a Gombe
- An bayyana su ne a wurin gangamin yakin neman zaben gwamna Inuwa Yahaya, wanda ke neman zango na biyu a 2023
- Sai dai duk da an yi sulhu tsakanin gwamna da Sanata Goje, ba'a ga sanatan ba a wurin kaddamar da kamfen yau Asabar
Gombe - Tsohon mataimakin gwamna a jihar Gombe, Charles Iliya, ya sauya sheƙa daga jam'iyyar PDP zuwa APC ranar Asabar 10 ga watan Disamba, 2022.
Jaridar Punch ta ruwaito cewa Iliya ya rike muƙamin mataimakin gwamna a zamanin mulkin Ibrahim Ɗankwambo.
Bayanai sun nuna cewa Charles Iliya ya kasance babbar ƙusa ga jam'iyyar PDP a shiyyar Gombe ta kudu kafin ya ɗauki matakin sauya sheƙa yau.
Daily Trust tace an bayyana shi a matsayin sabon mamban jam'iyyar APC a wurin gangamin fara yakin neman tazarce na jam'iyya mai mulkin jihar Gombe.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Daga cikin manyan sanannu kuma fitattun 'yan siyasan da suka sauya sheƙa a gangamin har da shugaban matasan PDP na shiyyar arewa maso gabas, Kabiru Jauro.
Tsohon shugaban matasan PDPn ya ɗau alƙawarin goyon bayan gwamna Muhammad Inuwa Yahaya a kokarinsa na ganin ya zarce zango na biyu a 2023.
Ta kama dole mu koma APC - Gwamna
Da yake jawabi a wurin taron, tsohon mai yi wa Atiku Abubakar Kamfe kuma tsohon ɗan takarar gwamnan PDP, Isyaku Gwamna, ya bayyana matakin koma wa APC a matsayin abun da ya zama dole.
Gwamna yace, "Ya fi kyau da nutsuwa ka dogara da zahiri fiye da ace ka zauna dogaro da abinda aka ɗaukar ma alƙawari."
Legit.ng Hausa ta gano cewa tsohon gwamna, Ɗanjuma Goje, wanda ke kan kujerar Sanatan Gombe ta tsakiya, shi ne kaɗai ɗan takarar da bai halarci taron ba.
Ba da jimawa ba Sanata Goje ya sasanta da gwamnan jihar Gombe tun bayan zaɓeen fidda gwanin APC wanda tsohon gwamnan ya lashe tikitin tazarce a kan kujerarsa.
Tsohuwar Ministar Ilimi a mulkin PDP ta goyi bayan Peter Obi
A wani labarin kuma Tsohuwar ministar ilmi, Dakta Obiageli Ezekwesili, tace ta gano wanda ya dace da mulkin Najeriya tsakanin manyan yan takara uku
Ezekwesili tave ta ganin ɗan takarar shugaban kasa na LP, Peter Obi, ba zata tsallake shi ta zabi wani ɗan takara daban ba a 2023.
A cewarta ta zauna ta baje abubuwan da ta sani kan kowane ɗan takara, ta gano cewa Peter Obi ya sha gaban sauran baki ɗaya.
Asali: Legit.ng