Kazantacciyar Halayyar da Aka Gani da Bidiyo Ba Shugaban APC Bane, Hadiminsa

Kazantacciyar Halayyar da Aka Gani da Bidiyo Ba Shugaban APC Bane, Hadiminsa

  • Hadimin shugaban jam'iyyar APC na ƙasa ya karyata bidiyon wani mutumi sintir ba tufafi wanda ake yaɗa cewa Adamu ne
  • Malam Muhammed yace waɗanda ke jingina wannan kazantaccen abun ga Abdullahi Adamu mutanen banza ne
  • Bidiyon ya nuna wani mutumin sintir babu tufafi a fadar mai martaba sarkin Lafiya

Abuja - Malam Nata’ala Mohammed, mai taimakawa shugaban APC na ƙasa kan harkokin midiya ya yi watsi da jita-jitar da ake yaɗawa cewa mutunin da aka gani a wani Bidiyo tsirara ana zargin Adamu ne.

Malam Muhammed yace zargin da ake cewa Adamu ne a bidiyon, wanda aka hangi wani Mutumin ya sabule kayansa zigidir a masaurautar Sarkin Lafiya ƙarya ne.

Sanata Abdullahi Adamu.
Kazantacciyar Halayyar da Aka Gani da Bidiyo Ba Shugaban APC Bane, Hadiminsa Hoto: vanguardngr
Asali: UGC

A wata hirar wayar tarho da Vanguard ta tattaro ranar Asabar a Keffi, Muhammed yace duk masu yaɗa wannan raɗe-raɗin basu da gaskiya kuma gurɓatattu ne.

Kara karanta wannan

Muna tare da CBN kan dokar kayyade cire kudi: Kungiyar Matasa

"Bidiyon dake yawo wanda ya nuna wani mutumi ya tuɓe zigidir ranar Alhamis, 8 ga watan Disamba a fadar mai martaba Sarkin Lafiya, wanda mutane ke zargin shugaban APC ne ƙarya ne."

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Kawai wani tunani ne na wasu gurɓatattun mutane waɗanda ba su san ainihin yadda surar Sanata Abdullahi Adamu take ba. Sun yi kuskuren dora lamarin kansa kuma ko ta wanne fanni bidiyon ba shi da alaƙa da Adamu."

- Malam Nata’ala Mohammed.

Wata ƙunguya ta yi Allah wadai

Haka zalika wata ƙungiya, A .A Sule Progressives Forum, ta fito ta yi Allah wadai da lamarin wanda ya haɗa da ɗaya daga dattawan ƙungiyar, Alhaji Abubakar Giza, mai sarautar Chiroman Giza.

Kodinetan ƙungiyar na jihar Nasarawa, Jonathan Samuel, ya ayyana lamarin da kazantacce kuma abinda ba za'a zuba ido a bari ya wuce haka nan ba, kamar yadda Daily Nigerian ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Ku Maida Takardun Kudi Mara Fenti Bankuna, Gwamna Ya Bayyana Abinda Zai Faru Nan Gaba

Ya bayyana cewa Giza dattijon arziki ne kuma babban jigo a jam'iyyar APC, sannan ya kasance ginshiƙi mai karfi wajen goyon bayan gwamnatin jihar Nasarawa.

"Ya zama wajibi a kwamuso duk masu hannu kan wannan mummunan halin a hukunta su don ya zama izina ga 'yan baya," inji Jonathan Samuel.

A wani labarin kuma Kotu Ta Kori Shugaban Masu Rinjaye Na Majalisar Dokokin Ebonyi Daga Takara a 2023

Rigingimun dake biyo bayan zaɓen fidda gwani sun yi awon gaba da tikitin neman tazarcen shugaban masus rinjaye na majalisar dokokin jihat Ebonyi.

Haka zalika Kotun ta ayyana Barsita Igboke a matsayin halastaccen ɗan takarar majalisar jiha na mazaɓar Ezza ta arewa maso yamma karkashin inuwar APC a zaben 2023.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262