Zaben 2023: Gwamna Ortom Ya Yi Muhimmin Hasashe Ga Jam'iyyar PDP

Zaben 2023: Gwamna Ortom Ya Yi Muhimmin Hasashe Ga Jam'iyyar PDP

  • Gwamnan Jihar Benue, Samuel Ortom, a ranar Laraba 7 ga watan Satumba, ya yi hasashen cewa PDP za ta lashe dukkan kujerun siyasa a jiharsa a zaben 2023
  • Gwamna Ortom ya ayyana a karamar hukumar Oju na jihar cewa PDP a Benue ba abin wasa bane
  • A cewar jigon na PDP wanda babban na hannun daman Gwamna Nyesom Wike ne, ya ce APC ta gaza a idanun yan Najeriya

Jihar Benue - Gwamna Samuel Ortom na jihar Benue ya yi imanin cewa jam'iyyar PDP ne za ta lashe dukkan kujeru a babban zaben 2023 da ke tafe.

Ortom ya yi wannan hasashen na alheri ne a ranar Laraba, 7 ga watan Disamba, yayin kaddamar da kamfe din yan takarar sanata a yankin Benue South da aka yi a Pavillion Square a karamar hukumar Oju, The Sun ta rahoto.

Kara karanta wannan

Jigon APC Da Ke Goyon Bayan Peter Obi Ya Bayyana Inda Za Su Koma Idan LP Ta Sha Kaye A 2023

Gwamna Ortom
Zaben 2023: Gwamna Ortom Ya Yi Muhimmin Hasashe Ga Jam'iyyar PDP. Hoto: (Photo: @GovSamuelOrtom)
Asali: Twitter

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Gwamnan, wanda ya yi ikirarin cewa jam'iyyar APC ta gaza a idanun yan Najeriya, ya ce PDP a jihar Benue ba abin wasa bane, Nigerian Tribune ta rahoto.

A jawabinsa ga magoya bayan PDP wurin taron, Ortom ya ce:

"Bari in fada muku cewa jam'iyyar PDP babban lamari ne a jihar Benue. Da izinin Allah, za mu lashe dukkan kujeru a zaben mu.
"Mu kungiya daya ce wadda ba za ta iya raba kanmu ba, kuma ta himmatu wajen ganin jam’iyyarmu ta PDP ta yi nasara, domin APC ta gaza a wannan kasa."

Gwamna Ortom ya bayyana sabbin tsare-tsare ga yan siyasa don warware matsalolin Najeriya

Gwamnan na jihar Benue, tunda farko ya yi kira ga dukkan shugabannin siyasa su tabbatar sunyi aiki tare don ceto Najeriya daga halin da ta ciki a yanzu.

Kara karanta wannan

Rikicin PDP: Magoya Bayan Atiku A Ribas Sun Aike Wa Wike Sako Mai Ƙarfi

Da ya ke magana jim kadan bayan karbar babban lambar karramawa a jihar, ta 'Grand Service Star of Rivers State GSSRS', a Fatakwal a ranar Asabar, 3 ga watan Disamba, ya bukaci yan Najeriya su yi watsi da son kai su yi aiki tare don nasarar kasar.

Wata sanarwa da babban sakataren yada labarai na Ortom, Nathaniel Ikyur ya fitar, wadda majiyar Legit.ng ta gani, ta ce a wannan lokacin a tarihin Najeriya da kasar ke fuskantar kalubale ta bangaren tattalin arziki, zamantakewa, siyasa da tsaro, abin da ake bukata shi ne mutane su nuna kishin kasa domin ceto kasar.

Ortom Ya Saka Sunan Wike A Layin Hanyar Zuwa Gidan Ayu

Gwamnonin G5 na PDP da ke tada kayan baya sai an tsige shugaban jam'iyyar na kasa, Iyorchia Ayu, sun halarci kaddamar da ayyuka da Gwamna Ortom ya yi a Benue.

A wurin taron, Ortom ya nada wa titin da ya yi wacce a bulle zuwa gidan Ayu, sunan Nyesom Wike na jihar Ribas.

Kara karanta wannan

Wata sabuwa: Dan takarar gwamnan APC ya ce zai yi amfani da baiwar 'Yahoo Boys'

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164