Jam'iyyar NNPP Mai Kayan Marmari Ta Fatattaki Shugabanta Na Kaduna Da Wani Babban Jami'i Kan Wasu Laifuka

Jam'iyyar NNPP Mai Kayan Marmari Ta Fatattaki Shugabanta Na Kaduna Da Wani Babban Jami'i Kan Wasu Laifuka

  • Jam'iyyar NNPP mai kayan marmari a jihar Kaduna ta fatattaki shugabanta, Ben Kure da mashawarci na shari'a Ibrahim Ahmed
  • An kori jami'an biyu ne bayan jefa kuri'ar rashin amanna a kansu da kwamitin ayyuka na jam'iyya ta yi a ranar 6 ga watan Nuwamba
  • An zargi Kure da Ahmed da laifuka daban-daban da suka hada da cin amanar jam'iyya, damfara, rashin gaskiya, zagon kasa, raba kan jam'iyya da wasu

Kaduna - Kwamitin ayyuka na jam'iyyar New Nigeria Peoples Party (NNPP) a Kaduna ta kada kuri'an rashin amanna kan Ben Kure da Ibrahim Ahmed, ciyaman da mashawarci na shari'a na jam'iyya.

Sakataren watsa labarai na jam'iyyar, Albehu Gora ne ya bayyana hakan ranar Talata a Kaduna cikin wata sanarwa da ya fitar, The Cable ta rahoto.

Kara karanta wannan

Jigon APC Da Ke Goyon Bayan Peter Obi Ya Bayyana Inda Za Su Koma Idan LP Ta Sha Kaye A 2023

Jam'iyyar NNPP
Jam'iyyar NNPP Mai Kayan Marmari Ta Fatattaki Shugabanta Na Kaduna Da Mashawarci Na Shari'a. Hoto: @thecableng.
Asali: Twitter

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Goro ya ce Kure da Ahmed sun saba tanade-tanaden da ke sasi na 31 na kudin tsarin jam'iyyar da sashi na 82(1), (3), (5) da sashi na 81(1) na dokar zaben kasa na 2022, rahoton Daily Trust.

Sanarwar ta ce:

"Kwamitin ayyuka na jam'iyyar NNPP na Kaduna ta yi taro a ranar 6 ga watan Nuwamban 2022 kuma bayan tattaunawa kan batun da mataimakin ciyaman Hon. Hosea Baba ya gabatar, tare da samun goyon bayan sakataren shirye-shirye, Alhaji Sa'ad Idris Kudan, sun cimma matsaya sun kada kuri'ar rashin amanna kan ciyaman din NNPP na Kaduna, Ben Kure, da mashawarci na shari'a, IB Ahmed.
"An cire tsohon ciyaman din da mashawarci na shari'a bayan korafe-korafe kan rashin yin ayyukansu, sakaci, saba dokar aiki, sabar dokar jam'iyya, rashin gaskiya, yaudara, raba kan kwamitin jam'iyya, zagon kasa, cin amanar jam'iyya da ka iya haifar da kiyayya, raini, rashin girmamawa da kunyata jam'iyya."

Kara karanta wannan

2023: Bola Tinubu Ya Ja Wa Kansa, Wani Babban Jigon APC Ya Fice Daga Jam'iyyar

Sanarwar ta cigaba da cewa:

"Ba sabon labari bane cewa a ranar 5 ga watan Oktoban 2022, tsohon mashawarcin na shari'a, bisa umurnin tsohon ciyaman din, ya nada tare da kaddamar da sabon mataimakin ciyaman na jam'iyya, ba tare da izinin ko ganawa da kwamitin shugabannin jam'iyya ba, hakan kuma ya ci karo da dokokin kundin jam'iyyar NNPP da dokar zabe na 2022."

Martanin Kure

Da aka tuntube shi domin ji ta bakinsa, Kure bai amsa kirar wata ba, kuma bai amsa sakon kar ta kwana da aka aika masa ba.

NNPP ta tafi kotu tana neman a haramtawa yan takarar APC shiga zaben 2023

A bangare guda, jam'iyyar New Nigeria Peoples Party a Kaduna ta shigar da kara kotu tana kallubalantar halascin 'yan takarar jam'iyyar APC a jihar gabanin zaben 2023.

NNPP tana son kotun ta haramta wa dan takarar gwamna da kuma yan takarar majalisun APC shiga babban zaben na 2023.

Kara karanta wannan

Daga Karshe Labour Party Ta Yi Martani Kan Dakatar Da Shugaban Kamfe Din Peter Obi, Ta Yi Magana Mai Muhimmanci

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164