Buhari Ya Nemi Sahalewar Majalisa Kan Nada Mataimakan Gwamnan Babban Banki

Buhari Ya Nemi Sahalewar Majalisa Kan Nada Mataimakan Gwamnan Babban Banki

  • Kowanne gwamnan babban banki dai ya na shafe shekaru hudu akan kujarar shugabancin bankin. Wanda kuma daga baya a kara masa ko kuma a sallameshi
  • Babban bankin kasa CBN, yana da mayan darakotoci da suke taimakawa gwamnan bankin wajen tafiyar da harkokin bankin
  • Shugaba Buhari ya turawa majalissar dattijai bukatar nada wasu daga cikin daraktoci da mataimaka ga gwamnan bankin

Abuja: Shugaban Kasa Muhammad Buhari ya bukaci majalisar dattawa da ta tantance tare da tabbatar da Edward Adamu Daraktan Sashen walwala na babban Bankin kasa CBN matsayin mataimakin gwamnan babban bankin.

Kazalika ya nemi majalisar da ta tabbatar da Aisha Ndanusa Ahmad mataimakiyar gwamnan babban bankin kasa CBN domin yin wa'adi na biyu a matakin, kuma wa'adin ta na karshe.

Kara karanta wannan

Badakalar N260m: Kotu Ta Yankewa Tsohon Shugaban Jami'ar Tarayya Ta Gusau shekaru 35 A Gidan Dan kande

Buhari
Buhari Ya Nemi Sahalewar Majalisa Kan Nada Mataimakan Gwamnan Babban Banki Hoto: The Nation
Asali: UGC

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shugaban Majalisar Dattawan, Ahmad Lawan ne ya karanta takardar a zauran majalisar. kamar yadda The Nation ta rawaito

A cewar wasikar, nadin nasu ta yi dai-dai da dokar aiki ta babban bankin kasa CBN ta shekarar 2007.

Sannan Shugaba Buhari, Ya bukaci majalisar dattawan data tabbatar da Ambasada Ayuba Ngbako na babban birnin tarayya a matsayin mamba na Hukumar tsarawa da raba haraji ta kasa (RMAFC).

Bugu da kari, Shugaba Buhari ya miki kundin kasafin kudin ayyukan babbar birnin tarayya ga majalisar domin amincewa kamar yadda kundin tsarin kasa ya tanadar karkashin sashe 121 a kundin tsarin mulkin kasa na shekarar 1999.

Babban Bankin Kasa Ya Sauyawa Wa Fasalin Kudin Nan Fasali

Babban bankin kasar nan ya kaddamar da sabbin faslin kudi a ranar 15 ga watan Nuwanban wannan shekarar.

Kara karanta wannan

EFCC Ta Kwato Dalar Amurka Miliyan 115 Daga Wajen Tsohuwar Ministan Mai Diezani

Sake fasalin dai ya biyu bayan kudirin gwamnatin shugaba Muhammadu buhari na inganta tattalin arzikin kasar nan da habaka kasuwanci kamar yadda gwamnatin ta sanar.

Ta kuma ce tayi haka ne dan maganin 'yan ta'adda da barayin gwamnati da suka tara kudi a gidajen su, suka hana su yawo a hanun mutane. Wannan matakin dai yasa mutane da dama sukar lamirin gwamnatin na yin hakan.

Masana da dama dai na fahimtar ba haka ya kamata ace gwamnatin tayi ba, kamata yayi ace ta fito da wani tsari da zai sa abun ya karbu ba tare da cutar da yan kasa ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel