Gwamna Masari Ya Mika Tutar APC Hannun Dan Takarar Gwamna a 2023

Gwamna Masari Ya Mika Tutar APC Hannun Dan Takarar Gwamna a 2023

  • Gwamna Masari na jihar Katsina ya damƙa tuta hannun ɗan takarar gwamna a inuwar APC, Dakta Dikko Umaru Radda
  • A ranar Litinin 5 ga watan Dismba, 2022, jam'iyyar APC ta kaddamar da yakin neman zaben ɗan takarar gwamna a Faskari
  • Jadawalin kamfen ya nuna jirgin Radda zai tashi zuwa Baure ranar Laraba, zai karkare ranar 26 ga watan Janairu a Funtuwa

Katsina - Gwamnan jihar Katsina, Aminu Bello Masari, ya miƙa Tuta ga baki ɗaya 'yan takarar jam'iyyar APC a jihar gabanin zuwan babban zaben 2023.

Gwamnan ya gabatar wa 'yan takarar Tutar ne a wurin kaddamar kamfen ɗan takarar gwamna, Dr. Dikko Radda, wanda ya gudana a Faskari ranar Litinin.

Channels ta tattaro ceqa yayin da yake karban Tutar daga Masari, Dakta Radda ya ɗau alkawarin tsare rayuka da dukiyoyin Katsinawa idan ya ci zaɓe mai zuwa.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Tsohon Kakakin Majalisar Wakilan Tarayya Ya Fice Daga APC, Ya Koma PDP

Katsina APC.
Gwamna Masari Ya Mika Tutar APC Hannun Dan Takarar Gwamna a 2023 Hoto: channelstv
Asali: Twitter

Ya kuma sha alwashin kula da Marayu da masu ƙaramin ƙarfi kana ya jaddada kudirinsa na inganta noma, lafiya, ilimi da kuma tallafawa matasa da mata domin kyaun gobensu.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

"Ba zamu baka kunya ba, haske ya samu gindin zama a jihar Katsina, kowa na iya banbance mai kyau da mummuna, haske da kuma dubu," Inji Radda.

Shugaban APC ya yaba da haɗin kan mutane

Tun da farko, shugaban APC na jihar, Sani Aliyu Daura, ya nuna gamsuwarsa da cincirindon mutanen da suka fito domin tarbar jirgin yakin neman zaɓen a ƙaramar hukumar Faskari.

Ya kuma bukaci Dakta Raɗɗa ya ɗauki kyawawan kudirorin Masari domin ciyar da jihar Kastina zuwa gaba. Ya roki baki ɗaya 'yan takarar su rungumi kamfen gida-gida don tabbatar nasarar APC tun daga sama har ƙasa.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Gwamnan Arewa Ya Lallaba Patakwal, Ya Sa Labule da Wike

Ya jaddada shirin jam'iyyar APC na ci gaba da zuba ayyukan romon demokaradiyya ga al'ummar Katsina ba tare da nuna banbanci ba don inganta rayuwa.

A jawalin kamfen, jirgin yakin APC zai matsa zuwa ƙaramar hukumar Baure dake shiyyar Daura ranar Laraba, 7 ga watan Disamba, kuma za'a cigab a da kewaye jihar har ranar 26 ga watan Janairu a Funtuwa.

Kamfen APC a Faskari.
Gwamna Masari Ya Mika Tutar APC Hannun Dan Takarar Gwamna a 2023 Hoto: Anas Jobe Aliyu/Facebook
Asali: Facebook

Tsohon ɗan takarar Kansilan Dabai, ƙaramar hukumar Ɗanja a Katsina, Usman Bandiro, wanda ya halarci taron, ya shaida wa Legit.ng Hausa cewa Katsina babu batun canza canji kowa ya bi.

Jigon APC yace al'umma sun fito kwansu da kwarkwata duk da yankin Faskari na cikin inda ake fama da matsalar rashin tsaro, "APC ta nuna banbanci idan aka yi la'akari da fitowar al'umma, Dikko na da masoya."

Haka zalika wani mamban APC ɗan tafiyar Gwagware We Know, wata ƙungiyar magoya bayan Dikko Raɗɗa yace wannan karon ba zasu yi sak ba a APC.

Kara karanta wannan

Jam'iyyar PDP Ta Sanar da Sakamakon Zaben Fidda Gwanin da Kotu Tace a Canza a Bauchi

Ɗan siyasan, wanda ya nemi a sakaya bayanansa yace Dikko ba shi da abokin hamayya sauran wasa suke, "Amma akwai wasu kujeru da zamu kauracewa APC."

Yakubu Dogara ya koma PDP

A wani labarin kuma Tsohon Kakakin Majalisar Wakilan Tarayya, Yakubu Dogara, Ya Fice Daga APC Ya Koma PDP

Awanni bayan ayyana goyon bayansa ga takarar Atiku Abubakar, Yakubu Dogara, ya tabbatar da barin jam'iyyar APC zuwa PDP a gangamin Legas.

Dogara, da wasu mambobin APC kiristoci a arewacin Najeriya sun ɗauri ɗamarar yakar tikitin Musulmi da Musulmi a matakin shugaban ƙasa, lamarin da ya hadda taƙaddama a APC.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262