Ministan Buhari Ya Fito da Lakanin da APC Za Tayi Amfani da Shi, a Doke PDP, LP da NNPP

Ministan Buhari Ya Fito da Lakanin da APC Za Tayi Amfani da Shi, a Doke PDP, LP da NNPP

  • Raji Babatunde Fashola yana cikin ‘yan gaba-gaba wajen yakin neman zaben Bola Tinubu a 2023
  • Ministan ayyuka da gidajen kasar yace ‘yan kwamitin takara za su shiga lungu domin tallata APC
  • Tsohon Gwamnan na Legas yana kokarin ganin ubangidansa ya gaji shugabancin Najeriya a badi

Abuja - Ministan ayyuka da gidaje a Najeriya, Raji Babatunde Fashola ya tabbatar da cewa jam’iyyar APC a dunkule take kan takarar Bola Tinubu.

A ranar Talata, 6 ga watan Disamba 2022, Daily Trust ta rahoto Babatunde Fashola yana bayanin hanyar da za su bi wajen kai jam’iyyar APC ga nasara.

Tsohon Gwamnan na jihar Legas yace za su rika shiga lungu, kwararo da sako domin su tallata takarar Asiwaju Bola Tinubu ga duk mutanen Najeriya.

Ministan shi ne yake rike da mukamin Darektan tuntuba da jawo mutane a kwamitin yakin neman zaben Tinubu/Shettima a karkasin jam’iyya mai mulki.

Kara karanta wannan

Atiku Abubakar: Abin da ya sa Bola Tinubu Ya Ruga Ingila, Ya Ji Tsoron Haduwarmu

Babatunde Fashola ya kaddamar da kwamitinsa

Babatunde Fashola ya yi wannan bayani a farkon makon nan, a wajen kaddamar da kwamitinsu.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

An rahoto Darektan kwamitin neman zaben yana mai sa rai Tinubu zai gaji Muhammadu Buhari wanda wa’adinsa zai cika a watan Mayun 2023.

Bola Tinubu
Bola Tinubu yana kamfe a Bayelsa Hoto: @officialasiwajubat
Asali: Facebook

Barr Mohammed Hassan Abdullahi ya wakilci Darekta

Mai girma Ministan muhalli na kasa, Barr Mohammed Hassan Abdullahi ya wakilci Babatunde Fashola a wajen rantsar da ‘yan kwamitin yakin zaben.

A madadin Fashola, Mohammed Hassan Abdullahi ya yi kira ga ‘yan kwamitin su dage wajen shiga ko wani sako da lungu domin su samu goyon baya.

Ministan kuma jigo a APC yana so a rage surutu, a dage da yi wa jam'iyya aiki.

Meke hana Tinubu zuwa taron 'yan takara?

Ana haka ne sai ga shi babban kwamitin yakin neman zaben ya wanke Bola Tinubu daga sukar da ake yi masa na kin halartar muhawara da abokan takara.

Kara karanta wannan

Olusegun Obasanjo Ya Nuna Inda Ya Dosa, Bai Goyon Bayan Atiku da Kwankwaso

A wani jawabi da Bayo Onanuga ya fitar, PCC yace a dokar kasa da tsarin mulki, babu inda aka wajabtawa ‘dan takara halartar taron masu neman mulki.

Premium Times tace Onanuga ya yi maganar ne biyo bayan ‘dan takaran na APC ya sake kauracewa zaman da gidan talabijin Arise TV ta shirya a Legas.

Dogara, Atiku da Wike

Rahoton da yake tashe a yanzu shi ne Gwamna Nyesom Wike ya ci karo da wanda ya yi masa kaca-kaca a rikicinsu da Atiku Abubakar a jam’iyyar PDP.

Rt. Hon. Yakubu Dogara wanda ya dawo PDP a makon nan ya jefawa Gwamnan kalubale, yana cewa zai fallasa sirrin zaman da suka yi kwanan nan.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng