Babu Kan ta a APC: EFCC Na Neman ‘Dan takaran Sanata a Kano a kan Zargin Damfara
- Hukumar EFCC mai yaki da masu yi wa tattalin arzikin Najeriya zagon ƙasa tana neman A.A Zaura
- Lauyoyin EFCC sun ce AbdulKareem AbdulSalam Zaura ya aikata laifin damfarar Dala miliyan 1.3
- Amma Lauyan da ya tsayawa ‘Dan siyasar yace babu dalilin da Jami’an EFCC za su fara farautar shi
Kano - A ranar Litinin, BBC Hausa ta rahoto cewa Hukumar EFCC mai yaki da masu yi wa tattalin arzikin Najeriya zagon kasa tana neman A.A Zaura.
EFCC tana karar Abdulkareem Abdulsalam Zaura wanda ya fi shahara da A.A Zaura da laifin satar Dala miliyan 1.3 a babban kotun tarayya da ke Kano.
Lauyan EFCC, Ahmad Rogha ya fadawa ‘yan jarida cewa wanda ake tuhumar ya ki kai kan shi kotu, don haka yace jami’an hukumar za su cafke shi.
Jawabin Lauyan EFCC
“Muna neman Abdulkareem Abdulsalam Zaura, za mu cafke shi da zarar mun kama shi''.
''A ƙa’ida, ya kamata a ce shi (A.A Zaura) yana hannunmu domin kotu ta tabbatar da haka.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Amma ina tabbatar da za a kama shi, a gurfanar da shi a gaban kotu a zamanta na gaba."
- Ahmad Rogha
Yaushe za a koma kotu?
The Guardian tace kotu ba ta iya zama a yau ba a dalilin wani taro da Alkalin shari’ar yake halarta a nesa. Ana sa ran nan da 'yan makonni a cigaba da shari'ar.
A ranar 30 ga watan Junairun shekarar badi, Mohammad Yunusa zai zauna domin cigaba da sauraron karar da ake yi tsakanin EFCC da attajirin ‘dan siyasar.
Lauya yace EFCC tayi kuskure
An rahoto Ibrahim Garba Waru wanda shi ne Lauyan ‘dan siyasar, yana sukar matsayar da EFCC ta dauka, yace babu dalilin cafke wanda ake tuhuma.
Ibrahim Waru yake cewa tun da dai kotu ba ta zauna a yau ba, bai kamata hukumar EFCC tace tana neman Abdulkareem AbdulSalam Zaura ruwa a jallo ba.
Kamar yadda wannan rahoto ya zo a The Cable, Lauyan yace ba dole ba ne Zaura mai takarar Sanata ya je kotun tarayyar tun da ana karar shi a kotun koli.
A cewar wannan Lauya, idan aka duba doka, jami’an EFCC ba su da hurumin cafke A.A Zaura. Zuwa yanzu jagoran na APC a jihar Kano bai yi magana ba.
Ganduje zai yi titi a Kwankwaso
An samu rahoto cewa Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya amince a kara makudan kudi domin a kammala titin Kwanar Kwankwaso-Kwankwaso a Madobi.
Baya ga haka, Gwamnan jihar Kano zai kashe N40, 373, 130.00 domin a gyara ban-daki da ake da su a wasu kasuwannin kauyuka da aka gina tun 2012.
Asali: Legit.ng