Daga Karshe Labour Party Ta Yi Martani Kan Dakatar Da Shugaban Kamfe Din Obi, Ta Yi Magana Mai Muhimmanci
- Dr Doyin Okupe har yanzu shine shugaban kwamitin yakin neman zaben dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar Labour Party
- Bayan dakatar da shi daga mazabarsa a jihar Ogun, jam'iyyar ta ce hanyar da aka bi wurin dakatar da shi ya saba da kundin ta
- Shugabannin jam'iyyar na kasa sun ce reshen ta na jihar Ogun ba su bi matakin warware rashin jituwa na jam'iyyar ba
FCT, Abuja - Shugabannin jam'iyyar Labour Party, LP, na kasa sun soke dakatarwar da sashin jam'iyyar na jihar Ogun ta yi wa Doyin Okupe, rahoton The Cable.
Da ya ke bayyana hakan a ranar Juma'a a Abuja, 2 ga watan Disamba, sakataren jam'iyyar na kasa, Umar Farouk, ya ce dakatar da aka masa ya saba kundin tsarin jam'iyyar.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Kamar yadda The Nigerian Tribune ta rahoto, Farouk ya bayyana cewa reshen jam'iyyar na Ogun ba ta bi dokokin da ya dace ba wurin dakatar da direkta janar na kwamitin yakin neman zaben.
Ya bayyana cewa Labour Party tana da tsare-tsare na yin sulhu a jam'iyyar, kuma reshen na jam'iyyar Ogun ba ta bi tsarin ba.
Farouk ya ce:
"Don haka dakatar da Dr Doyin Okupe daga reshen jam'iyya na Ogun ta yi bai da tasiri kuma har yanzu shi mamba ne mai kati na jam'iyyar Labour Party kuma direkta janar na kwamitin yakin neman zabe."
Ba ruwan kai a jam'iyyar Labour Party, In Ji Farouk
Kazalika, Farouk ya jadada cewa babu rabuwar kai a jam'iyyar yayin da ya ke karyata jita-jitar cewa akwai rabuwar kai.
Jam'iyyar za ta cigaba da goyon bayan Okupe a yayin da ya ke cigaba da jagorantar kwamitin yakin neman zaben.
Farouk ya ce reshen jam'iyyar na Ogun ba ta taba shigar da korafi a hukumance ba ga shugabannin jam'iyyar na kasa kafin dakatarwar da ta yi wa Okupe wanda ya saba wa doka.
Jam'iyyar LP Ta Ogun Ta Kori Shugaban Kamfe
Tunda farko, kun ji cewa jam'iyyar Labour Party ta jihar Ogun ta dakatar da shugaban kwamitin kamfen din shugaban kasa na Peter Obi da Datti Baba-Ahmed.
Shugabanin jam'iyyar na LP sun dauki matakin ne a garin Abeokuta, kan zarginsu da rashin biyan kudin wata-wata na jam'iyya da saba wasu dokokin.
Asali: Legit.ng