Farin Ciki Ya Zo Muku, Tashin Farashi Ya Zo Muku, Tinubu Ya Sake Kwafsawa a Wurin Kamfen

Farin Ciki Ya Zo Muku, Tashin Farashi Ya Zo Muku, Tinubu Ya Sake Kwafsawa a Wurin Kamfen

  • Dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar APC, Asiwaj Bola Ahmad Tinubu ya sake yin katobara a filin kamfen
  • Tinubu, tsohon gwamnan jihar Legas ya ‘tashin farashi ya zo nan’ wa jama’ar Bayelsa kafin daga baya ya gyara kalamansa
  • Ana ta nuna damuwa a Najeriya kan katobarar Tinubu a zance tun kafin ma ya lashe tikitin takarar APC

Yenagoa – Dan takarar shugaban kasa a jam’yyar APC, Asiwaju Bola Ahmad Tinubu ya sake kuren zance a ranar Alhamis 1 ga watan Disamba, inda ya danganta zuwansa da tashin farashi a jihar Bayelsa.

Ya bayyana hakan ne a gaban masoya da magoya bayan jam’iyyar a yayin taron kamfen da APC ta gudanar, kamar yadda rahotanni suka bayyana.

Da yake bayyana abin da ya kawo shi, Tinubu ya ce ya zo wa da mutanen jihar da fatan alheri da kuma ci gaba da ma farin ciki, amma ya kuskure ya fadi wata kalma mai gautsi.

Kara karanta wannan

Tinubu Ya Dawo da Komai Baya, Ya Fadi Gaskiyar Batun Haduwarsa da Gwamnonin PDP

Tinubu ya sake kwafsawa a filin kamfen
Farin Ciki Ya Zo Muku, Tsadar Kaya Ta Zo Muku, Tinubu Ya Sake Kwafsawa a Wurin Kamfen | Hoto: Vanguard News
Asali: Facebook

A cewarsa:

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

“Na kawo muku kyakkyawan fata, cewa farin ciki ya zo nan, cewa tashin farashi ya zo nan.”

Sai dai, da tuna ya kwafsa, sai ya gyara ya ce:

“Ya tafi”, magana tsadar kayayyaki a kasar a karkashin ikonsa sun kau.

Martanin ‘yan Najeriya ga kalaman Tinubu

Wasu ‘yan Najeriya da dama a shafin sada zumunta sun yi martani ga wannan kwafsi na Tinubu, ga dai abin da wasu ke cewa a shafin Twitter:

FS Yusuf ya ce:

“Ina ganin Bola Tinubu fa ya fada ma jama’ar Bayelsa gaskiya cewa “tashin farashi ya zo musu.” Don haka ba shi kuri’a daidai yake da ba karin farashin kayayyaki kuri’u.”

Lucky S. Oghuvwu yace:

“’Yan Najeriya ku waye fa. Tinubu ya ce, “FARIN CIKI YA ZO NAN, TASHIN FARASHI YA ZO NAN” wannan wani irin rudani ne? Ta yaya za a samu farin ciki ta hanyar tsadar farashi? Idan baku waye ba dukkanmu ne za mu dandana wahala. Bayan shekaru 8 na azabar Buhari, muna bukatar iska mai kyau mu shaka, don Allah.”

Kara karanta wannan

2023: Tinubu zai iya maida Najeriya ta zama sabuwa idan aka zabe shi, inji jam'iyyar APC

Blessing Emmanuel tace:

“A 2015 Buhari ya yiwa ‘yan Najeriya alkawarin daga SAMA har KASA, amma ‘yan Najeriya suka zabe shi.
“2022 Tinubu yana yiwa ‘yan Najeriya alkawarin TASHIN FARASHI, ina da yakinin tarihi zai maimaita kansa a 2023. ‘Yan Najeriya da tikar wahala kamar burodi ne da bota. Ba zan yi mamaki ba idan Tinubu ya ci zabe.”

A tun farko APC ta ce dan takarar da zai je Bayelsa don tallata hajarsa ta zaben 2023, ya kuma sakamako ya fito.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.