Kotu Ta Tabbatar Halascin Dan Takarar Gwamnan PDP a Jihar Ogun
- Babbar Kotun Abuja ta kawo karshen taƙaddama kan tikitin takarar gwamnan jihar Ogun karkashin inuwar PDP
- Da yake yanke hukunci mai shari'a Ekwo ya yi fatali da ƙarar wacce Jimi Lawal ya shigar bisa hujjar rashin gamsassun shaidu
- Kotun ta tabbatar da sahihancin zaben da PDP ta gudanar wanda ya samar da Oladipupo Adebutu a matsayin ɗan takara
Abuja - Babbar Kotun tarayya mai zama a Abuja ta tabbatar da Oladipupo Adebutu a matsayin wanda ya lashe zaben fidda gwani na takarar gwamnan jihar Ogun a inuwar PDP.
Channels tv tace Alkalin Kotun mai shari'a Inyang Ekwo shi ne ya bayyana haka yayin fatali da ƙarar da Jimi Lawal ya shigar, inda yace ba shi kwararan hujjoji gamsassu.
Lawal, wanda ya nemi takara a zaben fidda gwanin jam'iyyar PDP wanda ya gudana ranar 25 ga watan Mayu, 2022 ya kalubalanci nasarar Adebutu.
Ɗan takarar ya yi zargin cewa jam'iyyar PDP ta yi amfani da sunayen Deleget ɗin bogi waɗanda ba su ne na asali ba a lokacin gudanar da zaɓen.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Mista Lawal ya roki Kotun ta rushe zaben baki ɗaya sannan kuma ta tilasata wa jam'iyyar PDP shirya wani sabo tare da amfani da ainihin Deleget ɗin wucin gadi na asali.
Yadda Kotu ta yanke hukunci
Da yake bayyana hukuncin da Kotu ta yanke, mai shari'a Ekwo ya bayyana Lawal da "Baragurbi" kasancewar ya sauya sheƙa daga jam'iyyar APC zuwa PDP a watan Maris kuma ya nemi takara a zaben fidda gwanin da aka yi a watan Mayu.
Kotun ta yanke cewa sunayen Deleget ɗin da Lawal ke musu a kai, iri ɗaya ne da jerin sunayen da PDP da hukumar zaɓe mai zaman kanta watau INEC suka amince da su.
A cewar Alkalin wanna jerin sunayen ne aka yi amfani da su a wurin zaben fitar da ɗan takarar gwamnan, kamar yadda jaridar The Cable ta rahoto.
Ɗan Tsohon Gwamna Ya Lashe Zaben Fidda Gwanin APC Da Aka Canza a Ondo
A wani labarin kuma Ɗan tsohon gwamnan jihar Ondo, Adebayo Adefarati, ya lashe zaben fidda gwanin APC a wata mazaɓar ɗan majalisar tarayya
Jam'iyyar APC ta canza zaɓen fidda ɗan takarar ne bayan wasu daga cikin 'yan takara sun kai ƙarar jam'iyya Kotu, inda suka ƙalubalanci yadda aka gudanar da zaɓen a watan Mayu.
Sai dai yayin da kusoshin jam'iyyar suka sa baki aka zauna zaman neman maslaha kan taƙaddamar da ta kunno, sun cimma matsayar sake shirya wani, kotu ta basu wa'adin mako guda.
Asali: Legit.ng