Atiku Mashahurin Mayaudari Ne, Ya Fi Kowa Rauni a Cin Yan Takara, Oshiomhole

Atiku Mashahurin Mayaudari Ne, Ya Fi Kowa Rauni a Cin Yan Takara, Oshiomhole

  • Tsohon gwamnan Edo, Adams Oshiomhole, ya caccaki Atiku Abubakar yace sam ba abin yarda bane a 2023
  • Oshiomhole, mataimakin daraktan Kamfen Tinubu, yace Atiku rikakken mayaudari ne mai rauni a cikin yan takara
  • Gwamnonin jam'iyyar PDP da ake kira G5 ko tawagar gaskiya sun ce Atiku ba abin yarda bane

Tsohon shugaban APC na kasa, Adams Oshiomhole, yace ɗan takarar shugaban ƙasa a inuwar PDP, Atiku Abubakar, "Mashahurin ma ci amana ne" kuma "mafi rauni" a cikin 'yan takarar dake sahun gaba.

Mataimakin Darakta Janar na kwamitin yakin neman zaɓen Tinubu/Shettima, Oshiomhole, ya faɗi haka ne ranar Laraba yayin hira ta kai tsaye a Channels tv cikin shirin Politics Today.

Adams Oshiomhole da Atiku Abubakar.
Atiku Mashahurin Mayaudari Ne, Ya Fi Kowa Rauni a Cin Yan Takara, Oshiomhole Hoto: channelstv
Asali: UGC

Oshiomhole ya ƙara da cewa Atiku, "Shi ne mafi rauni daga ciki manyan 'yan takara uku dake sahun gaba," wanda suka haɗa da Bola Tinubu na APC da Peter Obi na Labour Party.

Kara karanta wannan

Shugaban Kasa a 2023: Idan Na Hau Kujerar Mulki Matasa Za Su Sha Romon Dadi, Atiku Abubakar

Tsohon gwamnan jihar Edo yace Atiku ba shi da hali mai kyau kuma ya rasa wurin zama idan aka yi la'akari yawon sauya sheka daga PDP zuwa ACN, ya sake komawa PDP ya shiga APC, daga karshe ya koma PDP.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

"Game da Atiku, da ace ba shi ne ɗan takara ba da yanzu ya sa kafa ya tafi Dubai. Amma kuna magana ne kan wani wanda daga barin Ofis ya koma goyon bayan matarsa maimakon ya tsaya ya taimaki kansa."
"Halayya abun duba wa ce, idan ka yarda da kanka ba zata riƙa tsalle-tsalle daga wannan jam'iyya zuwa waccan ba a kowane zaɓe."

- Oshiomhole.

Menene burin Atiku Abubakar?

A ruwayar The Nation, Tsohon gwamnan yace burin ɗan takarar PDP, Atiku na ganin ya zama shugaban kasa domin kansa ne kawai amma ba wai don son cigaban Najeriya ba.

Kara karanta wannan

2023: APC Ta Nesanta Tinubu da Wani Hoto da Ake Yaɗawa Tare da Shugaban Amurka, Ta Faɗi Gaskiya

Haka zalika yace bai kamata mutane su yi amanna da tsohon mataimakin shugaban ƙasan ba duba da yadda gwamnonin gidansa yan G5 ko tawagar gaskiya suka ƙi aminta da shi.

"Gwamnonin PDP da bakinsu suka ce ba zasu aminta da shi ba, duk wata yarjejeniya da muka ƙulla da shi ya karyata, rikakken mayaudari ne game da alƙawari."

APC Ta Hargitse a Jihar Jigawa Yayin da Wani Sanatan Jam'iyyar Ya Gana da Ɗan Takarar PDP

A wani labarin kuma mambobin APC sun shiga ruɗani bayan Sanata Sankara ya sa labule da ɗan takarar gwamnan Jigawa na PDP a Abuja

Sakamakon yadda ake zaman doya da manja tsakanin Sanata Ɗanladi Sanakara da kuma jagororin jam'iyyarsa APC a Jigawa, ana ganin wannan gana wa alama ce ta yana shirin sauya sheƙa.

An dai hangi mai neman zama gwamna a inuwar PDP, Mustapha Sule Lamido, ya garzaya har gidan Sankara a Abuja, sun yi kus-kus.

Kara karanta wannan

Rikicin PDP: Mun Tafka Babban Kuskure, Shugaban Kwamitin Yakin Neman Zaben Atiku Ya Magantu

Asali: Legit.ng

Online view pixel