Gwamna Abubakar zai nada wasu Kwamishinonin Jihar Bauchi
- Za a nada sababbin Kwamishinoni a Jihar Bauchi
- Yanzu an turawa ‘Yan Majalisar dokokin Jihar jerin
- Kwanaki aka zazzage mukarabban Gwamnatin Jihar
Mun samu labari daga Jaridar kasar nan cewa Gwamna Mohammed Abubakar zai nada wasu mukamai a Gwamnatin Jihar inda ya aikawa Majalisar dokokin Jihar sunayen kwamishinoni.
Shugaban masu rinjaye a Majalisar dokokin Jihar Tijjani Mohammed Aliyu da ke wakiltar Azare da Madangala ya bayyana haka a Majalisar a Ranar Talata. Honarabul Tijjani Aliyu yace Gwamnan ya aiko sunayen sababbin Kwamishinoni.
KU KARANTA: Wani Kwamishinan Bayelsa ya kife ana dakin taro
Gwamnan Jihar Abubakar ya aika sunayen Kwamishinoni 20 da ya ke sa ran Majalisa ta tantance su. A cikin sunayen da aikawa Majalisar akwai kowane mutum daga karamar Hukumar Jihar. Kwanaki Gwamnan ya sauke Kwamishinonin na sa.
Gwamna Abubakar ya bar Kwamishinan Ilmi na Jihar a mukamin sa wanda shi ne Mataimakin Gwamnan Jihar Injiniya Nuhu Gidado a matsayin sa. Gidado ya fito ne daga Yankin Jama’are. An dawo da wasu Kwamishinoni a cikin sabon jerin.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng