Gwamna Adeleke ya Bayar da Muhimmin Umarni ga Tsofaffin Jami’an Gwamnatin jihar

Gwamna Adeleke ya Bayar da Muhimmin Umarni ga Tsofaffin Jami’an Gwamnatin jihar

  • Gwamna Ademola Adeleke na jihar Osun ya umarci dukkan tsofaffin jami’an gwamnati da su dawo da kadarorin gwamnati dake hannunsu
  • Gwamnan a takardar da ya fitar ta hannun mai magana da yawunsa, yace kashi biyu bisa uku na kadarorin gwamnati tsofaffin ma’aikatan sun tafi dasu
  • Ya lissafa motoci, kwamfuyutoci da kayayyakin gidajen manyan jami’an gwamnati wadanda yace an yi awon gaba da su

Osun - Gwamnatin jihar Osun ta umarci dukkan tsofaffin jami’an Gwamnatin jihar da su dawo da kadarorin gwamnatin dake hannunsu a cikin sa’o’i 48, Channelstv ta rahoto.

Sanata Ademola Adeleke
Gwamna Adeleke ya Bayar da Muhimmin Umarni ga Tsofaffin Jami’an Gwamnatin jihar. Hoto daga channelstv.com
Asali: UGC

Mai magana da yawun Gwamna Ademola Adeleke, Olawale Rasheed, a wata takarda da ya fitar a ranar Laraba, yace wannan umarnin ya biyo bayan yadda ake waskar da kadarorin gwamnatin daga manyan jami’an gwamnatin da ta gabata ta Gboyega Oyetola.

Kara karanta wannan

FG Tace Gwamnatocin Jihohi ne Suke kara Tsunduma ‘Yan Najeriya Cikin Matsanancin Talauci

“Ababen hawa masu yawa sun yi batan dabo yayin da a rubuce an nuna cewa biyu bisa uku na tsofaffin jami’an gwamnatin sun tafi da ababen hawan ofisoshinsu.
“Da yawa daga cikin ma’aikatu da cibiyoyin gwamnatin an kwashe ababen hawansu, kwamfuyutoci da kayayyakin gidajensu. Gidajen wasu manyan jami’an gwamnati duk an cire musu hatta fitilu.”

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

- Takardar tace.

Rasheed yace duk wani tsohon jami’in gwamnati da ya ki bin wannan umarnin zai fuskanci fushin doka.

Adeleke, wanda aka rantsar a ranar Lahadin da ta gabata ya daskarar da dukkan asusun gwamnatin jihar kuma ya mayar da sunan jihar daga State of Osun zuwa Osun State.

Ya kara da dakatar da sarakuna uku na gargajiya tare da shugaban hukumar zabe ta jihar Osun.

Gwamna ya kori ma’aikata 12,000

A wani labari na daban, Sanata Ademola Adeleke na jihar Osun ya kori ma’aikata 12,000 kasa da sa’o’i 24 da hawansa karagar mulkin jihar.

Kara karanta wannan

Jiragen NAF Sun Ragargaji ‘Yan Ta’addan ISWAP Ana Tsaka da Koya Musu Hada Bama-bamai da Amfani da Makamai

Adeleke bai tsaya nan ba, ya tube rawanin sarakunan gargajiya uku na jihar da tsohon gwamnan ya nada.

Har ila Yau, Gwamnan ya dakatar da shugabannin kananan hukumomin jihar tare da dakatar da shugaban hukumar zabe na jihar.

Adeleke ya kara da dakatar da wasu manyan sakatarorin Gwamnatin jihar 30 da tsohon Gwamnan jihar ya ba aiki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng