Kano: Kotu Ta Yankewa Shugaban APC Hukuncin Daurin Shekaru 2 Kan Samunsa Da Katunan Zabe 376
- Shugaban jam’iyyar APC a gudunmar Yautar ya gurfana a gaban kotun majistare da ke zama a Kano
- Mai shari'a Faroukh Ibrahim Umar ya yankewa Aminu Ali hukuncin daurin shekaru biyu a magarkama kan samunsa da katunan zabe 376
- Kotun ta bashi zabin biyan tara na N500,000 kan tuhumar da ake masa na farko wanda tuni ya amsa laifinsa
Kano - Wata kotun Majistare ta Kano karkashin jagorancin Faroukh Ibrahim Umar ta yankewa shugaban jam’iyyar All Progressives Congress (APC), gudunmar Yautar, Aminu Ali, daurin shekaru biyu a gidan yari.
Hukuncin ya biyo bayan samunsa da aka yi da katunan zabe (PVC) guda 367 dauke da sunaye daban-daban, Daily Trust ta rahoto.
Jaridar ta rahoto cewa an kama Ali a watan Oktoba kan karbar katunan zabe daga wajen mutane daban-daban a karamar hukumar Gabasawa da ke jihar sannan cewa ya hada kai da wasu mambobin jam’iyyarsa wajen aikata laifin.
Kotu ta bashi zabin biyan tara
Kotun ta yanke masa hukunci bayan ya amsa laifinsa kan tuhume-tuhume biyu da ake masa, wanda yayi karo da sashi na 22 (a) na dokar zabe na 2022 kamar yadda aka gyara.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Sai dai kuma, kotun ta ba wanda aka hukuntan zabin biyan tara na N500,000 kan laifin farko rahoton Nigerian Tribune.
Kotun ta yanke masa hukuncin daurin watanni shida da zabin biyan tara N50,000 kan laifin hada kai da shi wajen aikata laifi, wanda ya sabawa sashi na 97 na dokar Penal Code.
An kama tsohon minista kan zargin lalata kayan APC
A wani labarin kuma, jami'an yan sanda a jihar Zamfara sun cika hannu da tsohon karamin ministan labarai, Aliyu Bilbis, bisa zargin hada kai da wasu wajen lalata allunan yakin neman zabe da wasu kayayyakin jam'iyyar APC.
Sai dai kuma, jam'iyyar PDP mai adawa ta zargi gwamnatin Bello Matawalle na jihar da yiwa 'ya'yanta dauki dai-dai tana kulle su saboda ziyarar da Dauda Lawan Dare, tsohon dan takararta ya kai jihar.
Sai dai har yanzu ba a samu kakakin rundunar yan sandan jihar, SP Muhammad Shehu a waya don jin ta bakinsa kan batun ba.
Asali: Legit.ng