Rudani Yayin da Fusataccen Sanatan APC Ya Gana da Dan Takarar PDP a Abuja

Rudani Yayin da Fusataccen Sanatan APC Ya Gana da Dan Takarar PDP a Abuja

  • Ɗan takarar gwamnan Jigawa a inuwar PDP, Mustapha Sule Lamido, ya gana da Sanata Danladi Sankara na jam'iyyar APC
  • Ganawar manyan yan siyasan biyu na Jigawa ya kaɗa hanjin 'ya'yan APC saboda Sanata Sankara ya nuna rashin jin daɗinsa tun a baya
  • Sai dai ana ganin ba zai sauya sheka daga APC ba saboda abokinsa na tsayin lokaci, Kashim Shettima, ya sa baki

Abuja - Taron da ya gudana tsakanin Sanata Danladi Sankara mai wakiltar mazaɓar Jigawa ta kudu maso yamma, da ɗan takarar gwamnan jihar karkashin PDP, Mustapha Lamiɗo, ya jefa waswasi a zuƙatan mambobin APC.

Jaridar Premium Times ta ruwaito cewa a ranar Litinin, 28 ga watan Nuwamba, 2022, manyan jiga-jigan siyasan biyu suka gana a sirrance a birnin tarayya Abuja.

Sankara da Mustapha Lamido.
Rudani Yayin da Fusataccen Sanatan APC Ya Gana da Dan Takarar PDP a Abuja Hoto: premiumtimes
Asali: UGC

Wannan na zuwa ne Kwanaki 5 bayan Sanatan ya ƙauracewa gangamin buɗe kamfen jam'iyyarsa ta APC da ya gudana a Gumel, ɗaya daga cikin kananan hukumomi 12 da suka haɗa mazaɓar Sanatan arewa/yamma.

Kara karanta wannan

Shehu Sani Ya Tona Asirin Abinda Yasa Ake Kai Hari da Ƙona Ofisoshin INEC Gabanin 2023

Sanata Sankara ya fara takun saƙa da gwamna Badaru na Jigawa gabanin zaben fidda gwani a shiyyarsa, ya zargi gwamnan da nuna wariya kuma ya janye daga shiga zaɓen.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Legit.ng Hausa ta fahimci cewa babu tabbacin yana da niyyar shiga PDP ko kawai ziyarar ta kai da kai ne da ya karbi bakuncin ɗan takarar gwamna na jam'iyyar adawa.

Bayan Sankara ya janye daga shiga tseren sake zama ɗan takarar Sanata na APC a jihar ya kuma yi fatali da tayin zama Darakta Janar na kwamitim kamfen APC a Jigawa.

Ganawarsa da ɗan takarar PDP ta zo ne lokacin da ake yaɗa jita-jitar Sanatan ka iya sauya sheƙa daga APC gabanin babban zaɓen 2023.

Wata majiya ta yi ikirarin cewa Mista Sankara ya zabi cigaba da zama a jam'iyya mai mulki ne sabida sa bakin abokinsa na tsawon lokaci kuma ɗan takarar mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima.

Kara karanta wannan

Rikicin PDP: Mun Tafka Babban Kuskure, Shugaban Kwamitin Yakin Neman Zaben Atiku Ya Magantu

Me suka tattauna a taron?

Mai neman zama gwamnan Jigawa a inuwar PDP, Mustapha Sule Lamido, yace ya gana da Sanata Sankara a gidansa dake Abuja a wani bangaren yawon neman shawarin da yake yi.

Ɗaya daga cikin hadimin Mista Lamido, Mansur Ahmad, yace Sankara na ɗaya daga cikin fitattun 'yan siyasa a Jigawa, waɗanda Uban gidansa ya nemi shawarinsu.

Sai dai Mansur Ahmad bai bayyana muhimman batutuwan da manyan 'yan siyasan biyu suka tattauna a taron ba.

2023: Mun Tafka Babban Kuskure a Rikicin PDP, Shugaban Kwamitin Kamfen Atiku

A wani labarin kuma shugaban kwamitin kamfen Atiku na ƙasa yace jam'iyyar PDP ta tafka babban kuskure a rikicin dake wakana da tsagin Wike G5

Shugaban kwmaitin kuma gwamnan jihar Akwa Ibom, Udom Emmanuel, yace dama ba za'a rasa 'yan kalubale a babbar jam'iyya lamba ɗaya Afirka ba watau PDP.

Gwamnan yace suna nan suka kokarin lalubo hanyar ɗinke barakar PDP kuma ana samun ci gaba, a cewarsa Atiku ne zai lashe zaɓen 2023.

Kara karanta wannan

Tashin Hankali: Wata Matar Aure, Maryam, Ta Sheke Kishiyarta Kan Abu Daya a Arewa

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262