Matasan Katsina Sun Yi Atiku Alkawarin Kuri'u Miliyan Shida a Zaben 2023

Matasan Katsina Sun Yi Atiku Alkawarin Kuri'u Miliyan Shida a Zaben 2023

  • Matasan Katsinawa karkashin ƙungiyar magoya bayan Atiku sun sha alwashin tattara wa jam'iyyar PDP kuri'u akalla miliyan 6
  • Kodinetan ƙungiyar, Yasir Ibrahim, ya faɗi haka ne a wurin rantsar da kodinetocin kananan hukumomi 34 a Katsina
  • Yace waɗanda aka zakulo aka baiwa mukaman zasu maida hankali wajen tabbatar da nasarar PDP a mazabunsu

Katsina - Matasa a jihar Katsina, arewa ta yamma, karkashin inuwar kungiyar Atiku Support Organization sun sha alwashin kawo aƙalla ƙuri'u miliyan Shida ga ɗan takarar shugaban kasa na PDP, Atiku Abubakar.

Channels tv ta tattaro cewa Kodinetan ƙungiyar na jiha, Yasir Ibrahim, ne ya faɗi haka a wurin taron rantsar da Kodinetocin ƙananan hukumomin Katsina 34.

Kungiyar masoyan Atiku.
Matasan Katsina Sun Yi Atiku Alkawarin Kuri'u Miliyan Shida a Zaben 2023 Hoto: channelstv
Asali: UGC

Taron rantsar da shugabannin ya gudana ne a Ofishin yaƙin neman zaben Atiku da ke birnin Katsina ranar Lahadi 27 ga watan Nuwamba, 2022.

Kara karanta wannan

Jam'iyyar PDP Ta Sanar da Sakamakon Zaben Fidda Gwanin da Kotu Tace a Canza a Bauchi

Yasir Ibrahim ya bayyana cewa waɗanda aka rantsar a matsayin Kodinetocin, masu shekaru tsakanin 30 zuwa 35, an naɗa su ne domin su tabbata Atiku ya lashe kowace rumfar zaɓe a kananan hukumomi 34 na Katsina.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ɗan takarar kujerar ɗan majalisar wakilan tarayya mai wakiltar mazaɓar Funtua da Ɗandume, Honorabul Rabilu Musa, ya halarci taron rantsarwan.

Honorabul Musa, wanda ya nuna gamsuwa da yanda matasa suka fito kwansu da kwarkwata a wurin taron, ya ce hakan ya tabbatar da cewa jam'iyyar PDP ce amsar da 'yan Najeriya ke nema.

Rigingimun jam'iyyar PDP

Legit.ng Hausa ta tattaro muku cewa jam'iyyar PDP ta jihar Katsina, inda shugaban ƙasa, Buhari, ya hito na fama da rikicin cikin gida har ta kai ga rabuwa gida biyu.

Tsagin ɗan takarar gwamna, Sanata Yakubu Lado Ɗanmarke da kuma tsagin tsohon shugaban jam'iyya, Alhaji Yusuf Majigiri, wanda ke da goyon bayan Ibrahim Shema, tsohon gwamna.

Kara karanta wannan

2023: APC Ta Hargitse a Jihar Arewa Yayin da Wani Sanatan Jam'iyyar Ya Gana da Ɗan Takarar PDP

Sai dai uwar jam'iyya ta ƙasa ta raba gardama kan shugabancin PDP a Katsina, inda ta naɗa Lawal Magaji Uli a matsayin muƙaddashin shugaba.

Legit.ng Hausa ta nemi jin ra'ayoyin wasu matasan Katsina harda waɗanda mambobi ne a jam'iyyar PDP kan wannan batu.

Umar Idris Dabai, makusancin ɗan takarar majalisar tarayya a mazabar Bakori/Ɗanja a inuwar PDP, Abdullahi Balarabe, ya faɗa wa wakilinmu cewa maganar gaskiya kokarin da suke Atiku ya ci Katsina.

A cewar Umar, idan ka duba mutane nawa ke da katin zaɓe a Katsina kuma ba kowane zai fito ya yi zabe ba, kuri'a miliyan 6 a matasa kaɗai da kamar wuya.

"Insha Allahu zamu yi iya bakin kokarinmu Atiku ya lashe Katsina, maganar alƙawarin kuri'u miliyan 6 dai zamu kokarta don naji labarin ƙungiyar," inji shi.

Wani mai suna Saifullahi Lawal, ya shaida mana cewa a zahirin gaskiya indai a tsakanin matasa ne maza da mata kuri'u miliyan shida ba zata haɗu ba.

Kara karanta wannan

Tashin Hankali: Wata Matar Aure, Maryam, Ta Sheke Kishiyarta Kan Abu Daya a Arewa

Matashin ɗan kimanin shekara 30 a duniya yace mutane sun gaji da APC don haka lokaci ya yi da suke da damar canza wa a 2023.

A wani labarin kuma Manyan 'yan takarar shugaban kasa biyu na sahun gaba sun kara yin naɗe-naɗe a kwamitin kamfen 2023

Mai neman zama shugaban kasa a inuwar APC, Ahmed Bola Tinubu, ya nada mai magana da yawun tawagar kamfe ta shiyyar arewa maso yamma.

Haka zalika takwaransa na jam'iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar, ya nada mai taimaka masa na musamman kan harkokin sadarwa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262