Manyan Kungiyoyin Magoya Bayan Atiku 10 Sun Koma Jam'iyyar APC

Manyan Kungiyoyin Magoya Bayan Atiku 10 Sun Koma Jam'iyyar APC

  • Kungiyoyin magoya bayan Atiku Abubakar sun jefar da kwallon mangwaro, sun koma jam'iyyar APC
  • Bayanai sun nuna cewa ƙungiyoyin guda 10 sun bar tafiyar PDP da Atiku ne saboda ba'a yaba musu tsawon shekaru
  • Gwamna Bello Matawalle ya nemi a saka su cikin tawagar yakin neman zaben Tinubu/Shettima

Zamfara - Ƙungiyoyin magoya baya 10 da suka yi mubaya'a ga ɗan takarar shugaban kasa a inuwar PDP, Atiku Abubakar, sun canza shawara, sun koma jam'iyyar APC, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.

Ƙungiyoyin da suka ɗauki matakin sun haɗa da, Atiku Support Organisation, PDP Transformation Ambassadors, Atiku Abubakar Kawai, PDP Mobilisers Initiative, Kasa Daya Al’umma Daya, da Atiku-Okowa Frontiers Movement.

Siyasar Najeriya.
Manyan Kungiyoyin Magoya Bayan Atiku 10 Sun Koma Jam'iyyar APC Hoto: punchng
Asali: UGC

Sauran su ne, G7 Business Community, Katsina Biyayya Forum, Atiku Women and Youth Initiative da kuma Atiku Nigeria Transformation Ambassadors, kamar yadda Punch ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Rabuwar Kan Kiristocin Arewa kan zaben 2023: Jerin wadanda suka kwancewa Babachir zani a kasuwa

Gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawalle da mataimakin shugaban APC na ƙasa na shiyyar arewa ta yamma, Salihu Lukman ne suka karɓi masu sauya shekar hannu biyu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yan siyasan sun rungumi APC ne a hukumance bayan wani taron gaggawa da ya kwashe awanni, a cewar wata sanarwa mai ɗauke da sa hannun kakakin APC na shiyyar arewa ta yamma, Musa Mailafiya Mada.

Sanarwar wacce ta samu haɗin guiwar sa hannun kakakin kwamitin kamfen Tinubu na shiyyar, Muhammed Shehu, ta ce:

"Waɗannan ƙungiyoyin sun sadaukar da kansu don goyon bayan Atiku da PDP amma aka yi watsi da su, sun zuba dukiyarsu da lokacinsu kan burin Atiku tun 2015 amma babu wani sakamako."
"Alaƙa mai tsamin da ta shiga tsakaninsu ya tilasta musu hijira daga PDP da ɗan takararta na shugaban kasa, kana suka ayyana mubayi'arsu ga APC da Bola Ahmed Tinubu."

Kara karanta wannan

2023: Atiku da Tinubu Sun Kara Shiri, Sun Yi Sabbin Naɗe-Naɗe a Kwamitin Yakin Neman Zabe

APC ta sanya kungiyoyin cikin kamfen Tinubu

Da yake karban 'yan siyasan a hukumance, gwamna Matawalle, kodinetan yakin neman zaben Tinubu/Shettima a arewa ta yamma ya bukaci a jefa ƙungiyoyin cikin kwamitin kamfe.

Gwamnan yace:

"Saboda haka ina kira gareku ku kara zage dantse ku haɗa da sadaukarwar da kuka yi tsawon shekaru wurin tabbar da nasarar APC da 'yan takararta tun daga sama har ƙasa."

A wani labarin kuma Manyan 'yan takarar shugaban ƙasa biyu da ake hasashen ɗayansu ne zai gaji Buhari sun yi sabbin naɗe-naɗe a kwamitin Kamfe

Atiku Abubakar ya nada mai ba shi shawara na muhamman kan harkokin sadarwa yayin da Bola Tinubu ya naɗa kakakin kwamitin kamfe na arewa ta yamma.

Sun ɗauki wanna matakin ne a wani bangare na kara karfin tawagar yakin neman zabe da kuma shirya wa zuwa babban zaɓen 2023.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262