Jerin Jiga-jigai, da gwamnonin Jam'iyyar APC 17 Da Suka Halarci Kamfen Tinubu Yau A Legas

Jerin Jiga-jigai, da gwamnonin Jam'iyyar APC 17 Da Suka Halarci Kamfen Tinubu Yau A Legas

Jiga-jigan jam'iyyar All Progressives Congress (APC) wanda ya hada da shugabannin jam'iyya, gwamnoni, kakakin majalisa, ministoci da sauransu sun yi gangami ranar Asabar a jihar Legas.

Jirgin yakin neman zaben Jam'iyyar ta APC ta yada zango mahaifarsa ta Legas a ranar Asabar, 26 ga watan Nuwamba, 2022.

Jiga-jigan sun taru ne a filin kwallon Teslim Balogun dake unguwar Surulere a Ikko.

Gwamnan jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu, wanda shine mai masaukin baki, ya bayyana cewa dan takaransu, Asiwaju Bola Tinubu, shine wanda ya cancanta a zaba, rahoton Tribune.

Ya bayyana cewa Tinubu zai maimaita irin nasararorin da ya samu a Legas idan ya samu damar mulkar Najeriya.

Gwamnan Kebbi, kuma shugaban kungiyar gwamnonin APC, Atiku Bagudu, ya bayyana cewa dukkan gwamnonin jam'iyyar 22 na tare da Bola Tinubu.

GWamnoni
Jerin Jiga-jigai, da GwamnoninJam'iyyar APC 22 Da Suka Halarci Kamfen Tinubu Yau A Legas Hoto: @APCPresCC2022
Asali: Twitter

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ga jerin jiga-jigan jam'iyyar da suka hallara:

 1. Gwamna Nasir El-Rufa'i na Kaduna
 2. Gwamna Abdulrahman Abdulrazak na Kwara
 3. Gwamna Adegboyega Oyetola na Osun
 4. Gwamna Babajide Sanwo-Olu na Legas
 5. Gwamna Dapo Abiodun na Ogun
 6. Gwamna Biodun Oyebanji na Ekiti
 7. Gwamna Simon Lalong na Plateau
 8. Gwamna Abdullahi Ganduje na Kano
 9. Gwamna Muhammad Badaru na Jigawa
 10. Mataimakin gwamna Babajide Hamzat na Legas
 11. Shugaban uwar jam'iyya, Abdullahi Adamu
 12. Sakataren Jam'iyya, Iyiola Omisore
 13. Tsohon Gwamnan Ogun, Segun Osoba
 14. Tsohon Gwamnan Borno, Kashim Shettima
 15. Tsohon Gwamnan Ogun, Gbenga Daniel
 16. Kakakin majalisar wakilai, Femi Gbaja
 17. Ministan Ayyuka, Raji Fashola

Kalli hotunan:

TInuub
Jerin Jiga-jigai, da gwamnonin Jam'iyyar APC 17 Da Suka Halarci Kamfen Tinubu Yau A Legas
Asali: Twitter

legas
Jerin Jiga-jigai, da gwamnonin Jam'iyyar APC 17 Da Suka Halarci Kamfen Tinubu Yau A Legas
Asali: Twitter

Tinubu Ya Sake Baranbarama, Ya Kira Katin Zabe PVC da APV-APC

Dan takara a zaben neman kujerar shugaban kasar Najeriya karkashin jam'iyyar All Progressives Congress (APC), Bola Ahmed Tinubu, ya sake baranbarama a wajen kamfe.

Yayin jawabi da gangamin mabiya dake wajen taro a filin kwallon Teslim Balogun, tsohon gwamnan na Legas yace su je su karbi katin "APV".

Yayinda yake kokarin gyarawa kuma ya sake tafka wata baranbaramar yace APC.

Dan takaran na APC ya kwan biyu yana subut-da-baka yayin jawabi ga jama'a a kwanakin nan.

A lokacin taron kamfen farko da APC ta gudanar da garin Jos, jihar Plateau, Tinubu ya yiwa jam'iyyar PDP addu'a maimakon APC.

Asali: Legit.ng

Online view pixel