Ko Shakka Babu Zan Kayar Da Peter Obi A Mahaifarsa Ta Anambra, Atiku
- Jam'iyyar PDP a Anamra tace yanzu haka tana da sama da kuri'u 500,000 wa dan takaranta, Atiku Abubakar
- Shugaban kamfen PDP a jihar yace a tarihi PDP bata taba fadi zaben shugaban kasa a Anambra
- Dan takaran shugaban kasan jam'iyyar Lp, Peter Obi, kuma haifaffen dan jihar ne, shin zai karya tarihin PDP?
Awka - Dan takaran kujerar shugaban kasa na jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Alhaji Atiku Abubakar ya bayyana cewa ko shakka babu zai lashe zaben jihar Anambra a 2023.
Wannan shine jawabinsa yayin zaman hada kan kungiyoyin magoya bayansa sama da guda 200 dake jihar karkashin jagorancin Dirakta Janar na kamfen Atiku-Okowa na jihar, Farfesa Obiora Okonkwo.
Okonkwo ya bayyana cewa ko shakka babu Atiku Abubakar da Ifeanyichukwu Okowa, zasu baiwa Peter Obi mamaki aFebrairun 2023, rahoton Tribune.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Ya ce:
"Ko shakka bamuyi jihar Anambara za ta baiwa PDP kuri'u mafi yawa; haka yake tun shekarar 1999. Bamu gushe jam'iyyar PDP duk da cewa wata jam'iyya ke mulkin jiha, amma mutane basu daina kadawa PDP kuri'u ba a zaben shugaban kasa."
"Kawo yanzu dai mun samu rahoton daga wajen mataimakin diraktan kungiyoyin mabiya, Hon. Onyebuchi Offor, cewa sama da kungiyoyin sa kai 200 masu mambobi sama da 500,000 ne daga runfunan zaben 5,720 a jihar aka taru."
Zamu ci Anambra, gida ce: Okowa
A riwayar Thisday, dan takaran kujerar mataimakin shugaban kasan PDP, Ifeanyi Okowa, ya ce jihar Anambra gida ce kuma ba ya tantama zasu lashe zaben jihar.
Yace:
"PDP ta shiryawa kamfe. Anambra tuni dama gida ce ga PDP, kuma kuje ku duba. A baya, mun lashe dukkan zaben shugaban kasa da tazara mai fadi. Muna kasance mafi rinjaye a majalisar dokokin jihar kuma ban tunanin komai zai canza yanzu."
"Kwamitin kamfen na nan zuwa Anambra, kuma zamu shiga kowani lungu da sako na jihar. Zamu taba ko ina, gunduma ne, karamar hukuma ce, har akwati."
"Ba na shakka ko kadan cewa al'ummar jihar Anamba zasu fahimci bukatar wakilai a Abuja. Kuma hanya daya da zasu samun hakan shine nasarar jam'iyyar PDP.
Asali: Legit.ng