2023: Tun da ‘Dan takaransa ya sha kashi, Buratai ya nuna wanda yake goyon baya
- Janar Tukur Yusuf Buratai yana ganin babu wanda ya cancanci a zaba a 2023 irin Asiwaju Bola Tinubu
- Dalilin tsohon shugaban rundunar sojojin kasa na bin bayan Tinubu shi ne Muhammadu Buhari
- Tukur Yusuf Buratai yace zai yi kyau jam’iyyar APC mai mulki ta cigaba da rike gwamnatin tarayya
Nasarawa - Laftanan Janar Tukur Yusuf Buratai mai ritaya, yana goyon bayan Asiwaju Bola Tinubu ya zama shugaban Najeriya a karkashin jam’iyyar APC.
A rahoton da Leadership ta fitar a ranar Juma’a, 25 ga watan Nuwamba 2022, an ji cewa Janar Tukur Yusuf Buratai yana tare da Bola Tinubu a zabe mai zuwa.
Jakadan na Najeriya a Jamhuriyyar Benin, ya nemawa ‘dan takaran na APC goyon bayan jama’a, inda ya yi wannan kira da ya ziyarci garin Keffi a Nasarawa.
Tsohon hafsun sojojin ya karbi kyauta na musamman daga wata kungiya ta tsofaffin Kansilolin Najeriya a kauyen Gora da ke cikin karamar hukumar ta Keffi.
Ya kamata a zabi Tinubu - Buratai
Da yake jawabi, Jakadan ya nuna ya shirya shiga siyasa da kyau, ya kuma roki mutane su kada kuri’a ga APC domin ganin gwamnatin nan ta zarce a mulki.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Rahoton yace Janar Tukur Buratai ya ambaci hako danyen mai a yankin Arewa maso gabas da canza kudin Najeriya a cikin nasarorin da aka samu a mulkin nan.
Saboda haka, Buratai yace akwai bukatar a samu shugaba nagari wanda zai iya cigaba da irin ayyukan cigaban da gwamnatin Muhammadu Buhari ta kawo.
Jakadan yace bangarori biyu da gwamnati mai-ci tayi fice su ne tsaro da gina abubuwan more rayuwa. An samu wannan labari ya zo a jaridar nan ta Pulse.
Duk da tsofaffin Kansilolin sun fito daga jam’iyyu dabam-dabam, Buratai ya nemi su duba nasarorin da aka samu a karkashin jagorancin APC daga 2015 zuwa yau.
A cewar tsohon sojan, sun samu tabbaci daga Bola Tinubu, don haka zai yi kyau a zabi jam’iyyar APC da ‘yan takaranta da Muhammadu Buhari yake goyon baya.
Bello Matawalle zai taimaki APC
Dazu an ji labari Gwamnan Zamfara yana cewa idan Asiwaju Bola Tinubu ya zama shugaban kasa a 2023, akwai damar mulki ya rika zagayawa a Najeriya.
Gwamna Bello Matawalle wanda shi ne shugaban kwamitin takarar Tinubu/Shettima a Arewa maso yamma zai ba APC gudumuwa a zabe mai zuwa.
Asali: Legit.ng