Gwamna Oyetola Ya Nada Sabbin Manyan Sakatarori 30 a Gwamnatinsa
- Gwamna Oyetola na jihar Osun ya zakulo mutane 30 daga ma'aikatan jiharsa ya naɗa su manyan Sakatarori
- Shugaban ma'aikatan jihar, Festus Iyebade, ne ya sanar da haka ranar Alhamis, yace zasu cike guraben da ake da su a bangaren
- Wannan na zuwa ne bayan gwamnan, mamban APC ya yi rashin nasara a zaben gwamnan da ya gabata a jihar a watan Yuli
Osun - Gwamnan jihar Osun, Adegboyega Oyetola, ya naɗa ma'aikata 30 a matsayin manyan Sakatarori a gwamnatinsa ranar Alhamis 24 ga watan Nuwamba, 2022.
Jaridar Punch ta ruwaito cewa sunayen mutanen da gwamna Oyetola na jam'iyyar APC ya naɗa na ƙunshe ne a wata sanarwa mai ɗauke da sa hannun shugaban ma'aikata, Dakta Festus Oyebade.
Sanarwan ta ƙara da cewa waɗanda Allah ya ci da aka naɗa su a matsayin manyan Sakatarorin zasu cike gurbin da ke akwai a sashin ma'aikatan gwamnatin jihar Osun, Daily Trust ta ruwaito.
Jerin sunayen waɗanda gwamnan ya naɗa
Legit.ng Hausa ta tattaro muku sunayen waɗanda wannan ci gaban ya shafa, sune kamar haka:
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
1. Injiniya Kamoru A. Babalola
2. Injiniya. S. O. Ajao
3. Mista M. A. K. Jimoh
4. Mista R. A. Popoola
5. Dakta D. O. Ogunrinade
6. Misi. J. K. Odediran
7. Mr. Oyesiku Adelu
8. Mista Babajide Falade
9. Misis Funmilola Oyewole
10. Mista O.A. Ogundun
11. Mista Bukola Aderibigbe
12. Mista Taiwo Oladunjoye
13. Dakta A. A Oni
14. Mista Lekan Babalola
15. Misis Sola Akinsola
16. Mista K.N. Akintola
17. Mista J. S. Adekomi
18. Misis Jibola Falode
19. Mis AY Esan
20. Misis C O Falade
21. Misis C O Fasina
22. Misis Gbemisola Fayoyin
23. Misis M. A Olawale
24. Mista S. A Raji
25. Kunle Adebayo
26. Mista T. O Akinwumi
27. Mista Richard Oyegbami
28. Mista Fatai Adekilekun
29. Mista M.O. Obidiya
30. Injiniya I. A Babalola.
Ku Yafe Mun Kura-Kuran da Na Tafka a Zamanin Mulkina, Masari Ya Roki Katsinawa
A wani labarin kuma kun ji cewa gwamna Masari na jihar Katsina ya roki al'umma su yafe masa idan ya yi kuskure a mulkinsa
Aminu Bello Masari, wanda zango na biyu na mulkinsa zai kare a watan Mayu, 2023, ya yi wannan roko ne a wurin kaddamar da kwamitin kamfe na Katsina.
Bugu da ƙari, gwamnan ya magana mai harshen damo inda yake cewa akwai wasu mutane duk abinda suka samu a gwamnatinsa ba su gode wa Allah ba.
Asali: Legit.ng