Kotuan Daukaka Kara Ta Maida Dan Takarar Gwamnan Taraba Na APC

Kotuan Daukaka Kara Ta Maida Dan Takarar Gwamnan Taraba Na APC

  • Kotun ɗaukaka ƙara ta tabbatar da ingancin zaɓen fidda gwanin APC a Taraba wanda ya ayyana Bwacha a matsayin ɗan takarar gwamna
  • Kotun ta jingine hukuncin babbar Kotun tarayya dake Jalingo, wanda ya rushe zaben fidda gwanin gaba ɗaya
  • Sanata Emmanuel Bwacha yace wannan nasara ce ga Demokuradiyya mutanen Taraba da APC

Yola, Adamawa - Kotun ɗaukaka kara dake zama a Yola, babban birnin jihar Adamawa, ta maida wa Sanata Emmanuel Bawachi takarar gwamnan jihar Taraba a inuwar jam'iyyar APC.

Da take yanke hukuncin, kwamitin alƙalai uku karkashin jagorancin mai shari'a Tani Yusuf Hassan, ta jingine hukuncin da Kotun baya ta yanke kana ta maida wa Bwacha takararsa a 2023.

Sanata Emmanuel Bwacha.
Kotuan Daukaka Kara Ta Maida Dan Takarar Gwamnan Taraba Na APC Hoto: Leadership
Asali: UGC

Leadership tace a ranar 20 ga watan Satumba, 2022, babbar kotun tarayya mai zama a Jalingo, jihar Taraba, ta rushe zaben fidda gwanin da ya ayyana Bwacha a matsayin ɗan takarar gwamnan APC.

Kara karanta wannan

Karin bayani: Kotun daukaka kara ta tabbatar da hukuncin dauri kan dan tsohon shugaban fansho

Biyu daga cikin 'yan takarar da suka fafata a zaben, Chief David Sabo Kente da kuma Sanata Abubakar Yusuf, ne suka ƙalubalanci nasarar Bwacha a gaban Kotu, sun zargi cewa an tafka maguɗi.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Sai dai a ruwayar Sahara Reporters, ranar Alhamis, Kotun ɗaukaka ƙara ta jingine hukuncin babbar Kotun. An ji lauyan APC na cewa gaskiya ce ta bayyana.

Lauyan, Boniface Iorkumbur yace, "An yi wa APC da ɗan takararta Bwacha adalci. Na yaba wa Alkalai a yanzun wanda nake kare wa da ɗan takararta zasu samu damar ci gaba da kamfe.

Sanata Bwacha ya yi martani

Da yake tsokaci kan hukuncin Kotun ɗaukaka ƙara ta wayar Salula, Sanata Bwacha yace wannan nasara ce ga demokaradiyya, mutanen Taraba da jam'iyyar APC.

Ta bakin mai magana da yawunsa, Mr. Reqwesin Muri, ɗan takarar gwamnan a inuwar APC yace wannan hukunci ya yi dai-dai da yadda aka gudanar da zaben fidda gwani a Taraba.

Kara karanta wannan

Da Duminsa: Kotun Daukaka Kara Ta Dawowa Binani Takararta ta Gwamnan Adamawa a APC

"Da muka saurari hukuncin Kotun Jalingo nun yi mamakin meyasa Alkalin ya rufe idonsa kan bayanan uwar jam'iyya ta ƙasa? Kuma kwamitin da ya shirya zaben ya kawo rahotonsa amma duk aka watsar."
"Muna godiya ga magoya bayan Sanata Bwacha, mambobin APC da masu watsa labarai bisa jajircewa har zuwa yau da gaskiya ta yi halinta."
"Ina mai ƙara jaddada wa mutanen jihar mu cewa Sanata Bwacha ya shirya tsaf kuma ya sadaukar da kansa wajen ceto Taraba daga gurɓatacciyar gwamnatin PDP idan ya lashe zaben 2023."

- Mista Reqwesin Muri.

A wani labarin kunji cewa Kotun ɗaukaka ƙara ta maida wa Sanata Aishatu Binani tikitin takarar gwamnan Adamawa a inuwar APC

Idan baku manta ba tun a watan Oktoba, 2022, babbar Kotun tarayya ta Yole ta rushe zaben fidda gwanin APC wanda Binani ta yi nasarar zama 'yar takarar gwamna a zaɓe mai zuwa.

Alkalin Kotun ya kuma yanke cewa jam'iyyar APC ta rasa takarar gwamna a jihar, lamarin da Sanatar tace ba zata saɓu ba, ta ɗaukaka ƙara zuwa gaba.

Kara karanta wannan

Gwamnonin Kudu Sun Sake Zama, Sun Yanke Wanda Zasu Goyi Bayan Ya Gaji Buhari a 2023

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262