Zaben 2023: Tinubu Ya Gamu Da Koma Baya A Yayin Da Manyan Yan APC 400 Suka Koma Bangaren Atiku

Zaben 2023: Tinubu Ya Gamu Da Koma Baya A Yayin Da Manyan Yan APC 400 Suka Koma Bangaren Atiku

  • Takarar shugabancin kasa na Bola Ahmed Tinubu ta sake cin karo da wani koma baya gabanin babban zaben 2023
  • Wasu manyan mambobin jam'iyyar APC a jihar Oyo a baya-bayan nan sun sauya sheka zuwa jam'iyyar PDP
  • Wani rahoto da ya fito ya tabbatar da cewa mambobin APC 400 ne suka sauya sheka zuwa PDP kuma suka yi alkawarin goyon bayan Atiku

Oyo, Ibadan - Jam'iyyar APC ta yi karo da lamari mara dadi a yayin da mambobinta fiye da 400 a jihar Oyo suka sauya sheka zuwa bangaren jam'iyyar hamayya ta PDP.

Kwamared Raji Akeem Kolaole, wanda ya jagoranci masu sauya shekan, ya bayyana cewa sun yi yi alkawarin goyon bayan Atiku Abubakar, dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP.

Tinubu da Atiku
Zaben 2023: Tinubu Ya Gamu Da Koma Baya A Yayin Da Manyan Yan APC 400 Suka Koma Bangaren Atiku. Hoto: Photo: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, Atiku Abubakar
Asali: Facebook

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Kara karanta wannan

Rikicin PDP: Na Hannun Daman Buhari Ya Shiga Kungiyar Gwamnonin G5, Ya Kulla Yarjejeniya Da Wike

Kamar yadda Daily Independent ta rahoto, Olubukola Olayinka, shugaban kungiyar goyon bayan Atiku/Okowa a jihar Oyo ne ta tarbi wadanda suka sauya shekar a ranar Talata, 22 ga watan Nuwamba.

Da ta ke magana da wadanda suka sauya shekar, Olayinka ya ce akwai babban aiki a gabansu, inda ta ce tafiya tasu na ceto Najeriya da yan Najeriya ne daga hannun masu 'nufin lalata kasa'.

Olayinka ta yi kira ga mambobi da magoya bayan jam'iyyar su cigaba da irin kamfen din da suka yi wa Atiku a yanzu.

Olayinka ta kuma ce:

"Kazalika, wannan sake sadaukarwa ne ga yan jam'iyyarmu na PDP da dama, a kananan hukumomi 33 na jihar Oyo kan takarar shugabancin kasa na Alhaji Atiku Abubakar bayan gano cewa shine kadai cikin yan takarar shugaban kasar da ke da kishin hada kan Najeriya da ceto kasa daga rugujewa da gwamnatin APC ta ingiza yan Najeriya."

Kara karanta wannan

Tinubu: Buhari ya jefa Najeriya a yunwa, amma ya yi wani abu 1 da ya kamat kowa ya sani

Wadanda suka sauya shekar sun bayyana dalilin barin Tinubu don Atiku

Kazalika, Akeem, wanda ya jagoranci masu sauya shekar ya ce APC ta gaza biya wa yan Najeriya bukatunsu kuma ta jefa kasar cikin mummunan hali, rahoton Daily Independent.

Kalamansa:

"Duk da cewa mun fara a matsayin yan PDP a 1998 kafin zaben 1999, mun koma APC a 2016, amma mun dawo gida ta sanadin Mayoress Olayinka saboda APC bata amfane mu ba a matsayin yan siyasa ko yan Najeriya.
"Bayan Moyoress Olayinka ta mana magana mu dawo gida, mun duba cewa ita mace ce mai kima da daraja da rikon amana a batun jagoranci da gaskiya."

Jigon Jam'iyyar PDP da Mambobi 200 Sun Koma APC

Wani cikin jiga-jigan jam'iyyar PDP mai mulki a jihar Delta, Prince Gabriel Nwanazia, ya koma jam'iyyar APC tare da wasu magoya bayansa 200.

Nwanazia, wanda ya tabbatar da koma wa APC a karamar hukumar Aniocha ta arewa tare da magoya bayansa, ya ce ya dauki matakin ne sakamakon rikicin PDP da ya ki ci ya ki cinye wa, rahoton The Punch.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164