Najeriya Ba Ta Yan Arewa Bane Su Kadai, Matasan Arewa Ga Dattawan Yankin

Najeriya Ba Ta Yan Arewa Bane Su Kadai, Matasan Arewa Ga Dattawan Yankin

  • Kungiyar matasan arewa ta yi martani ga bukatar dattijon yankin, Alhaji Zangon Daura da ya nemi a zabi dan arewa don ya gaji Shugaba Buhari a 2023
  • Shettima Yerima, shugaban kungiyar AYCF ya ce ba arewa kadai ke da Najeriya ba don haka akwai bukatar yin adalci a tsarin siyasar kasar
  • Yerima ya ce wannan ne ma babban makasudin da yasa gwamnonin APC daga arewa suka taru suka ce lallai a barwa kudu tikitin takarar jam'iyyar a zabe mai zuwa don cika alkawari

Gabannin babban zaben 2023, kungiyar matasan Arewa (AYCF) ta bayyana cewa Najeriya ba mallakin yankin arewacin kasar bane ita kadai.

Hakan martani ne ga furucin wani jigon kungiyar dattawan arewa, Alhaji Sani Zangon Daura wanda ya bukaci al’ummar arewa da su marawa dan takarar yankin baya, Nigerian Tribune ta rahoto.

Kara karanta wannan

Zaben 2023: Shin Atiku Zai Yi Sulhu Da Boko Haram? Ɗan Takarar Na PDP Ya Bayyana Abinda Ke Zuciyarsa

Yerima Shettima
Najeriya Ba Ta Yan Arewa Bane Su Kadai, Matasan Arewa Ga Dattawan Yankin Hoto: Daily Post
Asali: UGC

A cikin wata sanarwa da shugaban kungiyar matasan arewa na kasa, Yerima Shettima ya fitar, ya bayyana cewa goyon bayan dan kudu yana nuna adalci ne karara.

Najeriya ba ta yan arewa bane su kadai akwai bukatar yiwa kudu adalci

Ya bayyana cewa hakan ya kasance ne saboda Najeriya ba ta arewa bace ita kadai, ko Musulmai da Kiristocin arewa, yana mai cewa:

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

“Ko a kan tsarin kyawawan dabi’u, yawancin matakan siyasa da arewa ta dauka ya kasance kan hukuncin mika mulki a 2023, saboda shugabancin kasa ba zai zama gado ba kuma Najeriya ba ta mutum daya bace.”

Shettima ya ci gaba da cewar dattijon na fadin ra’ayin kansa ne kawai kuma hakan ba matsayin arewa gaba daya bane.

Ya ce:

“Akwai bukatar dan yin warwara a kan matsayin ubanmu Zangon Daura, hakazalika da ya yarda cewa dattawa abokan rakiya ne kawai ga matasa a yau.”

Kara karanta wannan

Shugabbanin Kudu Sun Koka Kan Yadda Aka Maida su saniyar Ware Musamman A Faggen Shugabancin

Kungiyar ta AYCF ta bayyana cewa a lokacin da gwamnonin arewa karkashin jagorancin gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-rufai suka lamuncewa dan takarar kudu don zama shugaban kasa, sun sha nanata batun adalcin siyasa

“Koda dai mu ba ‘ya’yan APC bane, mun yarda da batun cewa hukuncin na kan tafarkin adalci ga kudu a 2023.
“Muna kuma sane, haka kuma mahaifinmu Zangon Daura, cewa ana ganin mutuncin arewa kan cika alkawaranta ga kudu kuma wannan hali ne na daukacin yan arewa.
“Ba a sanmu da karya alkawara ba kuma wannan ya yi bayanin dalilin da yasa danmu, Shugaban kasa Muhammadu Buhari bai taba adawa da shawarar tsayar da dan takarar shugaban kasa dan kudu a jam’iyyar mai mulki ba. A arewa, kamar yadda mahaifinmu Zangon Daura ya sani, alkawara kebantattun abu ne kuma ma al’ada ne.”

A tuna cewa a wani faifan murya da ya ta yawo, an jiyo Alhaji Zangon Daura yana kira ga wata kungiya na matasa da su marawa dan arewa baya domin zama shugaban kasa a 2023, yana mai misali da tarihi da addini lamarin da bai kwantawa kungiyar AYCF ba, rahoton The Guardian.

Kara karanta wannan

Peter Obi ya tona sirrin gwamnoni, ya ce ba zai yi Allah wadai da wata kasurgumar kungiyar ta'addanci ba

Asali: Legit.ng

Online view pixel