Kotu Ya Umarci Jam'iyyar PDP Ta Canza Zaben Fidda Gwanin Sanata a Bauchi

Kotu Ya Umarci Jam'iyyar PDP Ta Canza Zaben Fidda Gwanin Sanata a Bauchi

  • Babbar Kotun tarayya a jihar Imo ta soke sakamakon zaɓen fidda gwanin PDP na mazaɓar Sanatan Bauchi ta kudu
  • Ta kuma umarci jam'iyya mai mulkin jihar ta shirya sabon zaɓen, hakan ta faru ne bayan wanda ya zo na biyu ya kai ƙara
  • Shugaban PDP na Bauchi, Alhaji Hamza Koshe Akuyam, ya ce jam'iyyarsu tana bin doka sau da ƙafa kuma zata yi biyayya ga umarnin

Bauchi - Babbar Kotun tarayya da ke zamanta a Owerri, jihar Imo ta umarci jam'iyyar PDP reshen jihar Bauchi ta shirya sabon zaɓen fidda gwani na takarar Sanatan Bauchi ta kudu.

A watan Mayu na wannan shekarar da muke ciki, PDP ta ayyana Garba Ɗahiru a matsayin wanda ya lashe zaben fidda gwani na mazaɓar Sanatan Bauchi ta kudu.

Hukuncin Kotu.
Kotu Ya Umarci Jam'iyyar PDP Ta Canza Zaben Fidda Gwanin Sanata a Bauchi Hoto: leadership.ng
Asali: Twitter

Jaridar Leadership ta rahoto cewa ɗan takarar da ya zo na biyu ya garzaya ya kai ƙara Kotu kuma ya yi nasarar samun umarnin tilasta wa PDP ta sake sabon zaɓe watanni kaɗan gabanin zaɓen 2023.

Kara karanta wannan

Asiri Ya Tonu: Wani Mutumi Ya Lakaɗa Wa Matarsa Duka Har Lahira Kan Karamin Saɓani

Ko ya jam'iyyar PDP ta ji da wannan hukuncin?

Da yake martani kan hukuncin da Kotu ta yanke, shugaban PDP na Bauchi, Alhaji Hamza Koshe Akuyam, yace jam'iyyar zata yi biyayya ga hukuncin babban Kotun tarayya ta Owerri.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Yace zasu bi umarnin Kotu da ya soke sakamakon zaɓen fidda gwanin da PDP ta shirya a mazaɓar Sanatan Bauchi ta kudu a babban zaɓe mai zuwa.

A cewarsa, jam'iyyar PDP jam'iyya ce mai bin doka sau da ƙafa kuma a shirye take ta yi abinda hukuncin Kotu ya umarci ta aiwatar.

Shugaban PDP a Bauchi yace:

"Eh, babbar Kotun tarayya ta umarci mu canza zaɓen fidda ɗan takarar kujerar Sanatan Bauchi ta kudu, ba wai soke zaɓen aka yi ba kamar yadda mutane ke yaɗa wa."

A wani labarin Rabiu Kwankwaso Ya Tsoma Baki a Rigimar Atiku da Gwamna Wike, Ya Tsagin G5 Suna da Gaskiya

Kara karanta wannan

Tinubi Ya Yi Gagarumin Rashi, Wani Shugaban APC da Wasu Jiga-Jigai Sun Fice Daga Jam'iyyar

Yayin da kadɗamar da wasu hanyoyin a jihar Ribas ranar Litinin, ɗan takarar shugaban ƙasa na NNPP yace tawagar gaskiya G5 suna yin abinda ya dace a rikicin PDP.

Tsohon gwamnan ya bayyana cewa ya bar PDP zuwa APC domin kawo wa Al'umma canji amma sai ya taras jam'iyyar ta zarce PDP lalacewa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel