El-Eufai Bai Ce Tinubu Ya Tsufa da Zama Shugaban Kasa Ba, APC Ta Yi Bayani
- An warware wani batu da ke yawo cewa, gwamnan jihar Kaduna, Mallam Nasiru El-Rufai ya ce Tinubu ya tsufa da zama shugaban kasa
- Warware wannan batu na fitowa ne daga bakin kakakin gangamin kamfen jam'iyyar APC a Arewa masu Yammacin Najeriya
- Muhammadu Shehu ya ce bidiyon da ake yadawa ba sabo bane, kuma wasu ne kawai ke kokarin kawo tsaiko ga APC
Kaduna - Jam'iyyar APC ta yi watsi tare da warware jita-jitan da ake yadawa a wani bidiyon da gwamnan Kaduna Mallam Nasiru El-Rufai wai ya ce Bola Tinubu bai cancanci gaje Buhari ba.
An ce El-Rufai ya ce sam Tinubu bai kamata ya yi takara ba saboda ya tsufa, lamarin da ya jawo cece-kuce a intanet.
Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa, kakakin gangamin APC a Arewa maso Yamma, Muhammad Shehu ya yi karin haske game da batun El-Rufa'i, inda ya ce kawai ana son hada fada ne a APC ta hanyar yada bidiyon.
Peter Obi ya tona sirrin gwamnoni, ya ce ba zai yi Allah wadai da wata kasurgumar kungiyar ta'addanci ba
Shehu ya yi gargadin cewa, ana ta yada bidiyon kafafen sada zumunta da ke nuna lokacin da El-Rufai ya yi maganar da ake cewa da Tinubu yake.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Yadda gaskiyar maganar take
Da yake warware batun, ya ce bidiyon da ake yadawan an gutsure shi, kuma an yi hira da gwamnan ne watanni da suka gabata, Within Nigeria ta tattaro.
A cewar Shehu, an tambayi gwamnan a hirar ne game da jita-jitan da ake yadawa na yiwuwar zama abokin takarar Tinubu, ko zama minista ko tsayawa takarar sanata.
Daga nan ne sai wasu 'yan adawa suka yi zaton ya nemi shugaban ma'aikatansa da ya ba shi tikitinsa na tsayawa takarar sanata.
Dan Tinubu ya shiga jerin matasa masu gangamin tallata mahaifinsa a jihar Kano
A wani kabarin kuma, hotuna sun nuna lokacin da dan Bola Ahmad Tinubu, dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar APC ya dura jihar Kano a shirin gangamin masoya APC.
An ruwaito cewa, Seyi Tinubu ya jagoranci matasa ne wajen tara mutane miliyan daya da ke kaunar APC da Tinubu a zaben 2023 mai zuwa badi.
Jam'iyyun siyasa na ci gaba da tallata 'yan takara gabanin 2023, ana ci gaba da musayar kalamai tsakaninsu.
Asali: Legit.ng