Zaben 2023: Kungiyar Ohanaeze Worldwide Ta Goyi Bayan Peter Obi, Ta Bada Dalili
- Takarar shugaban kasar Peter Obi ta samu karin tagomashi daga yankin kudu maso gabashin Najeriya
- A yayin da babban zaben shekarar 2023 ke karatowa, kungiyar Ohanaeze Ndigbo Worldwide ta goyi bayan takarar shugabancin kasar Obi
- Kungiyar ta dage cewa Obi ne mutumin da ya dace da aikin saboda adalci da daidaito, kuma a bawa tsohon gwamnan na Anambra dukkan goyon bayan da ya ke bukata don nasara a 2023
Ohanaeze Ndigbo Worldwide, kungiyar yan kabilar Igbo, ta jadada goyon bayanta ga Peter Obi, dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar LP.
Kungiyar tana da banbanci da Ohanaeze Ndigbo, karkashin jagorancin George Obiozor, The Cable ta rahoto.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Ohanaeze ta yi magana kan goyon bayan Obi don zama shugaban kasa
Emmanuel Iwuanyanwu, shugaban, dattawa na Ohanaeze, ya ce kungiyar ta yi imanin cewa goyon bayan Obi ne abin da ya dace, rahoton Blueprint.
Da ya ke magana a ranar Alhamis, 17 ga watan Nuwamba, a karshen taron kwamitin kudi da cigaba da kungiyar, Iwuanyanwu ya ce gamayyar ta kunshi shugabanni daga kudu maso gabas, kudu maso kudu da yankin tsakiya don goyon bayan Obi a babban zaben 2023.
Ya ce:
"Wasu da dama cikinsu har yanzu suna ganin lokaci ne na Igbo, kuma a hikimarsu, sun ce shugabancin kasa ya koma yankin kudu maso gabas.
"Sun cimma matsaya guda na goyon bayan Peter Obi, tabbas, mu Igbo a Ohanaeze muna farin ciki.
"Gaskiya shine Ohanaeze Ndigbo Worldwide na cikin wadanda suka amince kudanci da yankin tsakiya su goyi bayan takarar Peter Obi."
Ohanaeze ta bada dalilin goyon bayan takarar Obi
Ya ce zabin da suka yi na goyon bayan dan takarar shugaban kasar na LP ne saboda neman ganin adalci da daidaito a 2023.
Bidiyon Yadda Dandazon Mutane Suka Fito Ƙwansu Da Ƙwarƙwata Don Tarbar Peter Obi A Ya Fatawal Ya Ƙayyatar
A bangare guda, dan takarar shugaban kasa na LP, Peter Obi ya isa jihar Rivers, Fatakwal, don kaddamar da ayyuka masu muhimmanci da gwamnatin Gwamna Nyesom Wike ta yi.
A ranar Alhamis, 17 ga watan Nuwamban 2022, Obi zai kaddamar da gadan sama na Ikoku.
Tsohon gwamnan jihar Anambra, Peter Obi zai kaddamar da gadan sama na Nkpolu-Oroworoko (Ikoku) da gwamnatin jihar Rivers ta gina, bisa gayyatar mai girma gwamnan Rivers, Nyesom Wike.
Asali: Legit.ng