Lafiyar Tinubu, Asalinsa, Shekarunsa: Sanannen Dan Uwan Tinubu Ya Fasa Kwai Game Da Dan Takarar Na APC

Lafiyar Tinubu, Asalinsa, Shekarunsa: Sanannen Dan Uwan Tinubu Ya Fasa Kwai Game Da Dan Takarar Na APC

  • Jigo a iyalan su Tinubu, Olori Abi, ya yi karin haske game da shekaru, lafiyar da asalin dan takarar shugaban kasar na APC
  • Ade Ekemodu, shugaban iyalan na bangaren Sanusi na Iyalan Tinubu a Legas, ya ce tsohon gwamnan yana da lafiya kwarai da gaske
  • Olori na Ebi din ya ce idan aka yi gwajin kwayan hallita na DNA kan mai fatan zama shugaban kasar, sakamakon zai nuna shi haifafen dan iyalan Tinubu ne

Legas - Iyalan Tinubu, dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar APC, a Legas sun yi kira ga yan Najeriya su yi watsi da jita-jita da ake yada wa kan asali, lafiya da shekarun mai fatan zama shugaban kasar.

A cewar iyalinsa, dan takarar shugaban kasar haifafan da ne na gidan Tinubu a jihar Legas, The Guardian ta rahoto.

Kara karanta wannan

Tinubu Ya Tona Masu Lallaban Shi Wajen Samun Takarar Mataimakin Shugaban Kasa

Bola Tinubu
Lafiyar Tinubu, Asalinsa, Shekarunsa: Sanannen Dan Uwan Tinubu Ya Fasa Kwai Game Da Dan Takarar Na APC. @OfficialBAT
Asali: Facebook

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Menene batun lafiyar Bola Tinubu, dan takarar shugaban kasa na APC

Iyalan kuma sun ce lafiyar tsohon gwamnan na Legas bai da banbanci da duk na wani wanda ya haura shekaru 60, wanda ake kula da shi yadda ya dace.

Shugaban kwamitin shirye-shirye, Ade Ekemodu, ya yi kira ga yan Najeriya su bawa Tinubu dama ya gyara kura-kuren da aka yi a kasar, yana mai cewa a yanzu kasar tana wani muhimmin mataki ne.

Ekemodu, shugaban iyalan Tinubu bangaren Sanusi, ya ce yan Najeriya su bawa Tinubu dama a zaben shugaban kasa na 2023.

Su wanene iyalan Tinubu a Legas?

Babba a dangin ya tuna yadda dan takarar shugaban kasar ya farfado da tattalin arzikin Legas lokacin yana gwamnan jihar, da kokarinsa na kawo kudin shiga don yin ayyuka a jihar duk da cewa gwamnatin tarayya ta hana shi kason jihar.

Kara karanta wannan

A yi dai mu gani: Tinubu ya tara jama'a, ya yiwa Atiku da Peter tonon silili a Jos

Iyalan nasa sun bayyana cewa Tinubu lafiyarsa kalau kuma suka yi karyata jita-jita da ake yadawa cewa yana fama da rashin lafiya, rahoton Head Topic.

Wani sashi na sanarwar ta ce:

"Mutane suna ta magana kan cewa ko Tinubu ainihin dan gidan Tinubu ne ko a'a, ina magana ne a matsayi na na likita, idan ka yi gwajin DNA na Tinubu, za ka cewa sakamakon ya gasgata cewa shi dan gidan iyalan Tinubu ne. Ina magana a matsayin kwararre wanda ya yi shekaru 59 yana aiki."

Zaɓen Shugaban Ƙasa Na 2023: Jerin Buƙatun Da Shugabannin CAN Suka Gabatarwa Tinubu A Abuja

A gefe guda, kun ji cewa Bola Ahmed Tinubu, dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar APC, ya gana da shugabannin kungiyar kiristocin Najeriya, CAN, a birnin tarayya Abuja

CAN tunda farko ta nuna cewa ba ta goyon bayan tikitin musulmi na musulmi na jam'iyyar APC ta yi bayan zaben Kashim Shettima, tsohon gwamnan jihar Borno a matsayin abokin takararsa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel