Bidiyon Yadda Dandazon Mutane Suka Fito Ƙwansu Da Ƙwarƙwata Don Tarbar Peter Obi A Ya Fatawal Ya Ƙayyatar

Bidiyon Yadda Dandazon Mutane Suka Fito Ƙwansu Da Ƙwarƙwata Don Tarbar Peter Obi A Ya Fatawal Ya Ƙayyatar

  • Magoya bayan Peter Obi da aka fi sani da Obidients, sun tada kura a dandalin sada zumunta da sabon salon da suka bullo da shi
  • Hakan na zuwa ne a yayin da dandazon mutane, a ranar Alhamis, suka tarbi dan takarar shugaban kasar na LP, Peter Obi a Fatawal, babban birnin jihar Ribas
  • Gwamna Nyesom Wike ne ya gayyaci tsohon gwamnan na jihar Anambra zuwa jiharsa don kaddamar da wasu ayyuka da ya yi

Fatakwal - Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar Labour Party, LP, Peter Obi ya isa jihar Ribas, Fatakwal, don kaddamar da ayyuka masu muhimmanci da gwamnatin Gwamna Nyesom Wike ta yi.

A ranar Alhamis, 17 ga watan Nuwamban 2022, Obi zai kaddamar da gadan sama na Ikoku.

Peter Obi
2023: Dandazon Al'umma Sun Fito Yayin Da 'Obidients' Suka Tarbi Peter Obi A Fatakwal. Hoto: @PeterObi.
Asali: Twitter

Dandazon mutane sun yi wa Obi tarba ta arziki

Kara karanta wannan

Ana Tsaka da Rikici da Atiku, Wike Zai ba Peter Obi Gudumuwar Lashe Zabe a 2023

Tsohon gwamnan jihar Anambra, Mai girma Peter Obi zai kaddamar da gadan sama na Nkpolu-Oroworoko (Ikoku) da gwamnatin jihar Ribas ta gina, bisa gayyatar mai girma gwamnan Ribas, Nyesom Wike.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Dandazon mutane sun fito don tarbar Obi a Ribas.

Kalli bidiyon;

Wani mai amfani da Tuwita @Babz4elect, ya rubuta:

"Shugaban kasa na ya iso.
"Duba kauna da soyayya na ainihi, ba wasu da ke daukan hayan mutane ba da za su tarwatsa taron kafin a tashi.
@Peter Obi, ka yi wannan, mutanen Fatakwal, mun gode."

Yan Najeriya sun yi martani

Yan Najeriya sun tafi shafin Facebook na Legit.ng sun yi martani kan lamarin.

Engr Abednego John ya rubuta:

"Dan takara wanda ya cancanc aikin."

Kachi Kacheto ya ce:

"Ku bawa wannan babban mutumin hanya."

Kara karanta wannan

'Na Maka Magiya Dan Allah' Ɗan Takarar Shugaban Kasa Ya Roki Wike Ya Goya Masa Baya a 2023

Ikechukwu Godspower ya ce:

"Shugaban kasar mu mai jiran gado barka da zuwa birnin Fatakwal."

Ibrahim Movics ya ce:

"Muna cikin yanayi mai dadi
"Yaran Obidient ✅

Shedrack Nmaci ya ce:

"Muna gwada wannan makirfon din a PH tare da Wike, Obidients suna ko ina da ina. Peter Obi don shugaban kasa a 2023."

Dofe Nwannemo ya ce:

"Zabi Obi-Datti 2023, Jam'iyyar Labour Party!".

IGP Ya Bayyana Gwamnoni Na Ɗaukan Nauyin Kaiwa Abokan Hamayarsu Hari A Jihohinsu

Shugaban rundunar yan sandan Najeriya, Usman Alkali Baba ya yi zargin wasu gwamnoni ke daukan nauyin yan daba da ke kai hare-hare yayin kamfen din abokan hamayyarsu.

Shugaban yan sandan ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis 17 ga watan Nuwamba, yayin da ya ke magana da jam'iyyun siyasa da hukumar zabe mai zaman kanta INEC da masu ruwa da tsaki a zaben 2023, Leadership ta rahoto

Asali: Legit.ng

Online view pixel