Nafi Son a Kira ni da Baiwar Jama’a Fiye da ‘Yar Siyasa, ‘Yar Majalisa

Nafi Son a Kira ni da Baiwar Jama’a Fiye da ‘Yar Siyasa, ‘Yar Majalisa

  • Yar majalisar wakilai Nkiruka Onyejeocho daga jihar Abia, ta sanar da cewa tafi so a kira ta da baiwar jama’a a kan kiranta da ‘yar siyasa
  • Onyejeocha ta sanar da cewa ma’anar kalmar ‘dan siyasa tana nufin makaryaci, barawo da sauran miyagu dabi’u da ake ayyana su dashi
  • Ta sanar da cewa ta kai ga idan jama’arta suka bukaci wani aiki tace ba zata iya ba, suna cewa tayi musu alkawari saboda sun san bata sabawa

FCT, Abuja - Nkiruka Onyejeocha, mataimakiyar bulaliyar majalisar wakilai, tace tafi so a kira ta da “mai bautawa jama’a” saboda ita ba ‘yar siyasar zamani bace.

Honarabul
Nafi Son a Kira ni da Baiwar Jama’a Fiye da ‘Yar Siyasa, ‘Yar Majalisa. Hoto daga thecable.ng
Asali: UGC

A wata tattaunawa da tayi da manema labarai a ranar Talata a Abuja, Onyejeocha tace ana kallon ‘yan siyasa matsayin masu sata ko makaryata, jaridar TheCable ta rahoto.

Kara karanta wannan

Daya Daga Cikin ‘Yan Matan FGC Yauri da aka yi Garkuwa da ita ta Haihu a Hannun ‘Yan Bindiga

‘Yar majalisar tace ta bayar da gudumawa wurin ganin cigaban jama’arta tun daga lokacin da ta zaman kwamishina a jihar Abia.

“Wani abu mabanbanci shi ne ni ba ‘yar siyasa da aka saba gani bace, saboda kalmar ‘dan siyasa’ tana nufin wanda ya saba sata, karya, damfara da sauransu.”

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

- Tace.

Nafi don a kira ni da baiwar jama’a

“Toh kuwa hakan yasa nake sake tunani in ce ni ‘yar siyasa ce. Nafi so a kira ni da ‘hadimar jama’a’.
“Na sadaukar da kaina ga bautawa mazabata. Sun san ni wacece da kuma abinda na tsayawa. Ta kai matakin da idan aka nemi wani abu daga wurina kuma nace ba zan iya yi ba, sai su ce sai nayi musu alkawari. A lokacin da na nemi sanin abinda yasa, sai su ce saboda ina kiyaye alkawurrana.

Kara karanta wannan

Yadda Najeriya Tayi Mani Riga da Wando, Rabiu Kwankwaso Yace Ya Taki Sa’a a Siyasa

“Kafin in zama kwamishina a jihata, ina da mutane masu yawa dake karkashin shirin daukar nauyin karatun dalibai ‘yan jihar.
“A takaice, saboda taimakon jama’a da nake yi ne sarakunan gargajiya a karamar hukumata suka zabe ni don in zama kwamishina in wakilci karamar hukumata.”

- Ta kara da cewa.

Gogaggiyar ‘yar siyasar kuma ‘yar majalisar ta kara da cewa tana cigaba da kiyaye dokokin Ubangiji saboda bayan siyasa, zata yi bayani ga Ubangiji, jaridar TheCable ta rahoto.

Asali: Legit.ng

Online view pixel