Dalibar FGC Yauri da Aka Sace Ta Haihu a Hannun ‘Yan Bindiga

Dalibar FGC Yauri da Aka Sace Ta Haihu a Hannun ‘Yan Bindiga

  • Daya daga cikin ‘yan matan Kwalejin tarayya dake Birnin Yauri a jihar Kebbi da ‘yan bindiga suka sace ta haifa yaro namiji
  • Dalibar mai shekaru 16 wacce har yanzu ba a bayyana sunanta ba, ta kwashe sama da shekara daya a hannun ‘yan bindigan da suka sace su a watan Yunin 2021
  • Iyayen ‘yan mata sun koka kan yadda ‘yan bindigan suka kalmashe kudin fansa tare da aurar da ‘ya’yansu bayan garkuwa da suka yi dasu

Kebbi - Matashiyar budurwa mai shekaru 16 daga cikin daliban kwalejin tarayya dake Yauri a jihar Kebbi ta haihu a hannun ‘yan bindigan da suka yi garkuwa da su, jaridar PRNigeria ta rahoto hakan.

FGC Birnin Yauri
Dalibar FGC Yauri da Aka Sace Ta Haihu a Hannun ‘Yan Bindiga. Hoto daga thecable.ng
Asali: UGC

Dalibar tana daya daga cikin wadanda ‘yan bindigan suka sace a farmakin da suka kai makarantar cikin watan Yunin 2021.

Kara karanta wannan

Rashin Imani: ‘Yan Bindiga Sun Halaka Wanda Suka Yi Garkuwa Dashi, Suna Neman N10m na Fansar Gawarsa

Yadda aka sace daliban

‘Yan bindigan sun kutsa makarantar a babura inda suka budewa ‘yan sanda wuta tare da raunata wasu daliban yayin da mutum daya ya rasa ransa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Bayan kwanaki uku, a zagayen da sojoji suka yi, sun ceto uku daga cikin daliban yayin da aka sake ceto wasu biyu a watan Agustan 2021.

A watan Oktoban 2021, gwamnatin jihar Kebbi tace dalibai 27 da malamai uku da ‘yan bindigan suka sace sun shaki iskar ‘yanci.

Daliba ta haifa yaro namiji

Kamar yadda PRNigeria ta bayyana a ranar Lahadi, majiyoyi sun ce dalibar wacce ba a tabbatar da sunanta ba ta haifa yaro namiji a sansanin wadanda suka sace su a daji.

Iyayen dalibai sun shiga damuwa

Daya daga cikin majiyoyin sun ce, iyayen 11 daga cikin ‘yan matan dake hannun masu garkuwa da mutanen sun bayyana damuwarsu ganin cewa duk da an biya kudin fansa kuma an yi musayar fursunoni, har yanzu ba a saki ‘ya’yansu ba.

Kara karanta wannan

Dakarun Sojin Najeriya Sun Tarwatsa Sansanonin ‘Yan Bindiga, Sun Halaka 2 a Kaduna

“A yayin da gwamnati ballantana Atiku Bagudu, Gwamnan jihar Kebbi ya soke cinikayya da ‘yan bindigan wadanda suka bukaci kudin fansa, iyayen daliban da aka sace sun hada kudi tare da biyan na fansa domin sako ‘ya’yansu.”

- Wata majiya tace.

“Abun takaici ne yadda ‘yan bindigan suka karba makuden dukiya na fansa kuma suka aurar da wadanda suka sace tare da kin sakinsu.”

- Majiyar tace.

Asali: Legit.ng

Online view pixel