Akpabio Ya Sha Alwashin Garzayawa Kotun Koli Kan Hana Shi Takara

Akpabio Ya Sha Alwashin Garzayawa Kotun Koli Kan Hana Shi Takara

  • Tsohon ministan harkokin Niger Delta, Godswill Akpabio ya bayyana cewa zai tunkari kotun koli domin daukaka kara a hukuncin kotun daukaka kara
  • Ya bayyana cewa a matsayinsa na lauya, yana jiran kwafin shari’arsu sannan su san abinda ya dace su yi amma zasu je har kotun karshe
  • Akpabio yayi kira ga magoya bayansa, mambobin APC da ‘yan mazabarsa da su kwantar da hankali har zuwa lokacin da za a yanke hukuncin karshe

Uyo, Akwa Ibom - Tsohon ministan harkokin Niger Delta, Godswill Akpabio, yace zai tunkari kotun koli domin daukaka kara kan hukuncin kotun daukaka kara wacce ta soke zabenshi matsayin ‘dan takarar sanatan APC na Akwa Ibom a arewa maso yamma a zaben 2023.

Sanata Akpabio
Mummunan Gobara ta Tashi a Fitacciyar Kasuwar Singer Dake Kano. Hoto daga punchng.com
Asali: UGC

Akpabio wanda shi ne mataimakin shugaban kwamitin kamfen din shugabancin kasa na APC ya sanar da hakan a ranar Talata a Uyo, Punch ta rahoto.

Hukuncin da ya fatattaki Akpabio an yanke shi a ranar Litinin da yammaci a babban birnin tarayya.

“Hankalina ya kai ya hukuncin da kotun daukaka kada dake Abuja wacce tayi umarni ga INEC da ta cire sunana matsayin ‘dan takarar sanatan Akwa Ibom ta tsakiya a zaben 2023.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

“A yayin da nake jiran kwafin shari’ar, akwai amfani inda bayyana cewa ni lauya ne kuma ‘dan kasa mai biyayya ga doka da hukuncin kasar nan da suka fito daga kotu.
“Lauyoyina sun fara duba hukuncin domin sanin abinda zamu yi a hukumance. Na san cewa kotun koli ce ke da hukuncin karshe a wannan lamarin.”

- Yace.

Ya kara da cewa:

“A don haka nake shawartar magoya bayana, mambobin APC da dukkan ‘yan mazabu na da su kwantar da hankalinsu kuma su kasance masu biyewa doka yayin da suke cigaba da yakin ganin nasarar APC a Akwa Ibom ta arewa maso yamma, Akwa Ibom da Najeriya.”

Hukuncin daukaka kara

Kotun daukaka kara dake zama a babban birnin tarayya dake Abuja a ranar Litinin ta fatattaki Sanata Godswill Akpabio matsayin ‘dan takarar sanatar Akwa Ibom ta arewa maso yamma.

A hukuncin kotun, tace matsayin Akpabio ‘dan takara a zaben fidda gwani na shugaban kasa na APC, bai samu damar shiga zaben fidda gwanin da INEC tayi ba na yankin a ranar 28 ga watan Mayu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel