Shugaba Buhari, Gwamnoni da Sanatoci Sun Dira Jos Yayin da Tinubu Zai Bude Kamfen 2023
- Jos, babban birnin jihar Filato ta cika maƙil ba masaka tsinke yayin da APC ke gangamin kaddamar da kamfen Tinubu
- Tuni dai shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ya dira birnin, inda ya taras da gwamnoni suka rankaya zuwa filin taron
- Bayanai sun nuna cewa Filin ya cika taf da mutane, matar Tinubu da matar abokin gaminsa Shettima na filin Ruwang Pam Township Stadium
Jos, Plateau - Shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, da manyan jiga-jigan jam'iyyar AOC yanzu haka sun taru a Jos, babban birnin jihar Filato domin kaddamar da kamfen din Bola Tinubu.
Legit.nga Hausa ta tattaro cewa yanzu haka ana ci gaba da harkokin kamfe a filin Ruwang Pam Township Stadium, Jos, wanda ya cika ya batse da mutane.
Tun da farko, wasu daga cikin gwamnonin APC ne suka tarbi shugaban ƙasa Buhari, daga nan suka rankaya tare zuwa wurin da aka shirya gangamin.
Mai taimakawa shugaban kasa kan harkokin sadarwar zamani, Bashir Ahmad ne ya sanar da isar Buhari a shafinsa na Tuwita.
Rahotanni sun bayyana cewa an hangi aƙalla gwamnonin jam'iyyar APC mai mulki guda 10 a wurin taron.
Wasu hotuna daga Jos
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Gwamnan jihar Filato, Simon Lalong ne mai tarbar baƙi kuma shi ne darakta Janar na kwamitin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na jam'iyyar APC a 2023.
Jam'iyyar APC ba ta fara yaƙin neman zaɓen Tinubu da Shettima da wuri ba sakamakon taƙaddamar da ta barke kam mambobin kwamitin kamfe na farko da aka fitar.
Gwamnoni ne suka fara kukan cewa an yi watsi da mutanensu, lamarin da ya haddasa Gwamna Lalong yace za'a sake nazari don shawo kan komai kafin fara kamfen.
Sanatan PDP ya yaba wa Bola Tinubu
A wani labarin kuma Sanatan PDP ya fito fili ya yaba wa wasu nasarori da ɗan takarar shugaban ƙasa na APC ya samu a Legas
Sanata Chimaroke Nnamani daga jihar Enugu kuma tsohon gwamnan jihar yace Tinubu ya taka rawar da dole a yaba masa lokacin yana matsayin gwamnan Legas.
Yace Jagoran APC na ƙasa ya taka muhimmiyar rawa gagara misali wajen tsaftace da inganta ayyukan bangaren shari'a daga 1999 zuwa 2007 a jihar Legas.
Asali: Legit.ng