Gwamna Wike Ya Gayyaci Buhari, Peter Obi, Oshiomhole, Da Sauran Jiga-Jigai Don Kaddamar da Ayyuka a Jiharsa

Gwamna Wike Ya Gayyaci Buhari, Peter Obi, Oshiomhole, Da Sauran Jiga-Jigai Don Kaddamar da Ayyuka a Jiharsa

  • Gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike ya bayyana gayyatarsa ga manyan Najeriya don kaddamar da wasu ayyuka jiharsa
  • Gwamnan na PDP ya gayyaci shugaba Buhari da dan takarar shugaban kas ana jam'iyyar Labour Peter Obi
  • Hakazalka, ya gayyaci sarkin Kano da wasu jiga-jigan siyasar kasar nan ciki har da wadanda ba 'yan jam'iyyarsa ba

JIhar Ribas - Shugaban kasa Muhammadu Buhari da dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar Labour, Peter Obi na daga jerin wadanda aka gayyata don bude wasu ayyuka a jihar Ribas.

Gwamna Nyesom Wike na PDP ne ya bayyana wannan gayyata ga jiga-jigan siyasar kasar nan yayin da yake ci gaba da kai ruwa rana tsakaninsa da shugabannin PDP.

Wannan na zuwa ne cikin wata takardar sanarwar kaddamar da ayyukan da jaridar Tribue Online ta samu a ranar Litinin 14 ga wata Nuwamba.

Kara karanta wannan

2023: Kada Yan Najeriya Su Cire Rai, APC Zata Kawo Canjin da Suke Bukata, Tinubu

Gwamna Nyesom Wike ya gayyaci Buhari ya bude wasu ayyuka a jiharsa
Gwamna Wike Ya Gayyaci Buhari, Peter Obi, Oshiomhole, Da Sauran Jiga-Jigai Don Kaddamar da Ayyuka a Jiharsa | Hoto: blueprint.ng
Asali: UGC

A cewar jaridar, za a kaddamar da ayyukan ne daga ranar 14 ga watan Nuwamba zuwa 2 ga watan Disamba, kuma an gayyaci manyan shugabanni da dama na Najeriya, ciki har da Buhari, Obi, Oshiomole da dai sauransu.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Wuraren da za a kaddamar a Ribas

Daga ayyuka 16 da za a kaddamar, ciki har da aikin da ya ci biliyoyin kudade na fannin lafiya da ilimi, wanda tuni Buhari ya ba gwamnan lambar yabo bisa aikata su.

Shugaba Buhari, wanda zai samu wakilcin daya daga hadimansa zai kaddamar da makarantar lauyoyi ta Nabo Graham Douglas da Wike ya gina a Fatakwal a ranar 18 ga watan Nuwamba.

Obi kuwa, zai kaddamar da aikin gadar sama ta Nkpolu-Oroworokwo a Fatakwal a ranar 16 ga watan Nuwamba.

Shi kuwa Adams Oshiomole, na gaba-gaba a kamfen Tinubu, zai kaddamar da gadar sama ta Rumepirikom a ranar 15 ga watan Nuwamba.

Kara karanta wannan

Rikicin PDP: Ban Rufe Kofar Sulhu Ba, Atiku Ya Bawa Wike Amsa

Sarkin Kano ya samu gayyata daga Wike

Hakazalika, Wike ya gayyaci sarkin Kano, HRH Nasiru Ado Bayero, inda zai kaddamar da wata katafariyar cibiyar kiwon lafiya da jinyar sankaran jini da aka yiwa sunan Dr Peter Odili.

Alkalin alkalan Najeriya kuwa, zai kaddamar da wani aikin cibiyar shari'a ta Mary Odili, kamar yadda rahoton Blue Print ya bayyana.

A bangare guda, sufeto janar na 'yan sandan Najeriya, zai kaddamar da cibiyar 'yan sanda ta fannin binciken sirri a jihar.

Gwamna Wike dai na ci gaba da kai ruwa rana da shugabannin PDP, inda yake bayyana bukatar korar shugaban PDP na kasa Iyochia Ayu.

An ruwaito cewa, tsohon shugaban kasa Janar Ibrahim Badamasi Babangida zai sulhunta rikicin da ke tattare da PDP gabanin babban zaben 2023.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.