Maza Sun Dade Suna Mulkin Najeriya, Lokaci Ya Yi da Mata Za Su Karbi Ragamarta, Inji Dan Takara Sowore
- Dan takarar shugaban kasa, Omoyele Sowore ya bayyana ra'ayinsa game da mata su rike ragamar mulkin kasar nan
- Sowore ya bayyana cewa, mata sun fi yawa a Najeriya, akwai bukatar su samu damar rike ragamar kasar
- Hakazalika, ya ce sam a Najeriya ba a yiwa mata adalci, akwai bukatar a basu damar nuna kwarewa da bajintarsu
Najeriya - Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar AAC, Omoyele Sowore ya shawarci mata da su tada jijiyar wuya tare da tashi tsaue wajen karbe ragamar mulkin kasar nan kasacewar maza sun dade suna mulkarta, Daily Trust ta ruwaito.
Dan gwagwarmayar ya bayyana hakan ne a ranar Lahadi yayin tattaunawar bayyana ra'ayoyi da Arise Tv tare da hadin gwiwar cibiyar habaka dimokradiyya ta CDD suka shirya.
Sowore ya kuma bayyana kokensa ga yadda aka mai da mata saniyar ware duk da kuwa su ne mafi yawa a kasar.
Mata sun fi yawa a Najeriya, akwai bukatar su tashi tsaye su karbi mulki, inji Sowore
A cewarsa:
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
"Akwai mata a kasar nan da suka cancanci kada kuri'u fiye da maza. Shin yaushe mata za tsayar da mata, su kada musu kuri'u, sannan su tursasa mazajensu su zabi mata? Wannan ne zai warware batun daidaito a lokaci guda.
"Dalilin da yasa nake fadin haka, Najeriya na da ma'aikatar harkokin mata. Ban taba jin ma'aikatar harkokin maza ba.
"Akwai wani lokaci, inaga a FCT ne lokacin da namiji ya nemi a zabe shi a matsayin shugaban mata. A Adamawa, an taba yin kwamishinan harkokin mata kuma namiji."
Ba a yiwa mata adalci, inji Sowore
Sowore ya kuma bayyana cewa, ba adalci bane ba mata 35% na kujerun gwamnati, inda ya shawarce su da su tashi tsaye su nemi kari, Sahara Repoeters ta ruwaito.
Ya kuma yi tsokaci da cewa, a Najeriya, mata ne 51%, yayin da maza ke daukar 49%, amma mata ba sa samun manyan kujeru a kasar masu yawa.
A wani labarin kuma, shugaban jam'iyyar APC na kasa ya ce, Tinubu ne zai gaji Buhari, kuma yana da yakinin hakan a zaben 2023.
Ya kuma shaidawa Tinubu cewa, ya fara shirin fara aiki a matsayin shugaban kasa nan ba da dadewa.
Asali: Legit.ng