Keyamo, Dino Melaye Sun Yi Wa Peter Obi Izgili A Yayin Da Magoya Bayansa Ke Faɗa Akan Rabon Kuɗi
- Magoya bayan jam'iyyar Labour Party sun saba yi wa kansu kirari da cewa ba su bada 'sisi' wato kudi ga magoya baya
- Sai dai a wani bidiyo da ya bazu a dandalin sada zumunta, an hangi mutane sanye da riguna masu tambarin Labour Party na fada kan rabon kudi a Abia
- Kakakin kwamitin takarar shugaban kasa na APC Festus Keyamo da na jam'iyyar PDP Dino Melaye sun yi wa Obi izgili kan bidiyon
Festus Keyamo, mai magana da yawun kwamitin kamfen din dan takarar shugaban kasa na APC, da Sanata Dino Melaye, kakakin kwamitin yakin neman zabe na dan takarar shugaban kasa na PDP, sun yi wa Peter Obi, dan takarar shugaban kasa na Labour Party izgili, kan bidiyon magoya bayansa da ke fada da juna, rahoton Daily Trust.
A wasu bidiyon da ke yawo a dandalin sada zumunta, an ga wasu mutane suna zanga-zangar cewa ba su samu kasonsu da aka musu alkawari ba saboda halartar babban taron Labour Party a jihar Abia.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Obi ya halari jihar a ranar Alhamis don kaddamar da kamfen din Alex Otti, dan takarar gwamna na jam'iyyar.
Bayan dan takarar shugaban kasar ya tafi, bidiyon mutane sanye da riguna masu tambarin jam'iyyar Labour Party ya bazu a dandalin sada zumunta.
An jiyo wani mutum yana cewa:
"Nawa za su bamu a nan?"
Abin da Keyamo ya ce
Da ya ke martani, Keyamo, wanda shine karamin ministan ayyuka, a wani sakon rubuta ya rubuta:
"Masu cewa ba su bada sisi' suna fada kan 'sisi' 'Za ka iya rudar mutane wasu lokotan, za ka iya rudar dukkan mutane wani lokacin, amma ba za ka iya rudar dukkan mutane a dukkan lokuta ba' .... Abraham Lincoln."
Martanin Melaye
Dino Melaye, shima a bangarensa ya tofa albarkacin bakinsa kan bidiyon a shafinsa na Twitter.
Ya ce:
"Jam'iyyar Labour ta Obi na karyar cewa ba sisi amma duba abin da suke yi wurin kamfen a Abia. Yaudara da makaryata."
Bidiyon ya janyo cece-kuce a dandalin sada zumunta.
APC: Abubuwa 3 da Suka Hana a Ga Bola Tinubu a Taron ‘Yan Takaran Shugaban Kasa
Kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa na jam’iyyar APC ya fitar da jawabi a kan rashin halartar taron da aka yi da masu neman mulki.
A wata sanarwa da ta fito daga bakin Festus Keyamo, SAN, an ji cewa Bola Tinubu yana da wasu abubuwan da suka hana shi zuwa taron jiya da aka yi.
Asali: Legit.ng