Tinubu Ya Yi Alkawarin Karasa Aikin da Aka Yi Shekara 43 An Gaza Kammalawa a Arewa

Tinubu Ya Yi Alkawarin Karasa Aikin da Aka Yi Shekara 43 An Gaza Kammalawa a Arewa

  • Asiwaju Bola Tinubu ya yi alwashin ganin kamfanin Ajaokuta ya tashi da kafafunsa a mulkinsa
  • ‘Dan takaran ya shaidawa masu aikin hako ma’adanai cewa zai yi amfani da su wajen habaka GDP
  • Muddin APC tayi nasara a zaben 2023, Gwamnatin Bola Tinubu za ta hada-kai da masu hannun jari

Nasarawa - A yayin da ‘Dan takaran APC, Asiwaju Bola Tinubu ya zauna da masu hako ma’adanai a garin Lafiya, a jihar Nasarawa, ya yi masu alkawari iri-iri.

This Day tace Asiwaju Bola Tinubu ya sha alwashin ganin gwamnatin tarayya ta kammala aikin kamfanin Ajaokuta wanda tun a shekarar 1979 aka gina shi.

Gwamnatoci da-dama sun yi makamancin wannan alkawari, har yau abin ya faskara.

‘Dan takaran shugaban kasar ya shaida cewa gwamnatinsa za ta hada-kai da masu hannun jari domin ganin an farfado da tattalin arziki idan ya samu mulki.

Kara karanta wannan

Tinubu: Mun Samu Dabarar da Za Mu Bi Wajen Lahanta Kwankwaso a Arewa Inji PCC

Ma'adanai za su babbako tattalin arziki

Tinubu yace masu hako ma’adanan kasa za su ba Najeriya irin gudumuwarsu idan har ya ci zabe.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A 2020, gudumuwar bangaren ma’adanai ga karfin tattalin arzikin Najeriya bai kai 1% ba, ‘dan takaran shugaban kasar yace gwamnatinsa za ta kawo sauyi.

Tinubu
Bola Tinubu a Lafia Hoto: @officialasiwajubat
Asali: Facebook

Kamar yadda rahoton ya zo mana, da yake jawabi a ranar Alhamis, Tinubu yace zai bunkasa tattalin arziki ta yadda za a samu cigaba, a daina zaman banza.

A bangaren amfani da kayan gona, The Nation tace Tinubu yace gwamnatinsa za ta hada-kai da majalisa a kawo dokoki, kuma a zauna da masu hannun jari.

"Gwamnatina za ta tabbatar da cewa an kammala kamfanin karfe na Ajaokuta har ya fara aiki ta karkashin tsarin hadin gwiwa na PPP.
A fannin juya kayan gona, gwamnatina za ta cigaba da kokari, mu maida hankali wajen cigaban kamfanoni domin kara yawan abinci.

Kara karanta wannan

Tsohon Shugaban EFCC Ya Ga Tinubu a Aso Rock, Ya Ambaci Abin da Zai Taimaki APC

Kuma hakan zai taimakawa manomanmu da kamfanoni su kara samun darajar dukiyarsu."

- Bola Tinubu

Tinubu ya ci zabe - Ribadu

Rahoton nan yace tsohon shugaban hukumar EFCC yana ganin da wahala a samu ‘dan takaran da zai iya doke Bola Tinubu a cikin masu neman mulki.

Masu fashin bakin siyasa suna ganin cewa wadanda za su kawowa Tinubu kalubale a zaben badi su ne; Atiku Abubakar, Peter Obi da Rabiu Kwankwaso

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng