Tinubu Ya Sha Alwashin Samar da Ayyuka 1m a Shekaru 2 na Farkon Mulkinsa

Tinubu Ya Sha Alwashin Samar da Ayyuka 1m a Shekaru 2 na Farkon Mulkinsa

  • Bola Ahmed Tinubu, ‘dan takarar shugabancin kasa na jam’iyyar APC ya sha alwashin samar da ayyuka miliyan 1 a shekaru 2 na farkon mulkinsa
  • ‘Dan takarar shugabancin kasan ya sha alwashin zai farfado da masana’antu, tallafawa mata da matasa tare da farfado da tattalin arziki
  • A taron da aka yi a Abuja yayin bayyana manufofinsa, Tinubu yace zai dakile hauhawar farashin kayayyaki da kalubalen tattalin arziki a Najeriya

Abuja - ‘Dan takarar shugabancin kasa na jam’iyyar APC, Bola Ahmed Tinubu, yayi alkawarin samar da ayyuka miliyan daya a shekaru biyu na farkon mulkinsa, jaridar The Nation ta rahoto.

Bola Ahmed Tinubu
Tinubu Ya Sha Alwashin Samar da Ayyuka 1m a Shekaru 2 na Farkon Mulkinsa. Hoto daga thenationonlineng.net
Asali: UGC

Tsohon gwamnan jihar Legas, Otunba Femi Pedro ya bayar da wannan tabbacin a Abuja yayin da yayi bayanin manufofin Asiwaju Bola Ahmed Tinubu a wani taro a Abuja.

Kara karanta wannan

Rabin Albashi: Badaru Ya Bayyana Kokarin da Suke Tsakanin ASUU da FG

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Kamar yadda Pedro ya bayyana, Tinubu yana da manufofi 12 muhimmai na tattalin arziki domin fitar da Najeriya daga halin matsin tattalin arziki da suka shiga.

Sauran manyan lamurran tattalin arziki da Tinubu yace zai tabbatar sun hada da:

  • Farfado da kamfanoni da masana’antu da suka dade da mutuwa a kasar nan
  • Tallafawa mata da matasa
  • Kara fadada samar da kayan ababen more rayuwa tare da
  • Dakile hauhawar farashin kayayyaki a kasar nan.

Tuni APC ta kafa Kwamitin Yakin neman zabe

Tuni jam’iyyar APC ta fitar da sunayen tawagar yakin neman zaben shugaban kasa inda da farko lamarin ya rincabe tare da kawo rikicin cikin gida a jam’iyya.

Bayan wasu kwanaki da fitar da sunayen ne aka sake fitar da sabbin sunaye wanda aka saka wasu daga cikin masu korafin tare da cire wasu.

Kara karanta wannan

Tinubu Ya Yi Alkawarin Karasa Aikin da Aka Yi Shekara 43 An Gaza Kammalawa a Arewa

Tawagar yakin neman zaben ta hada da ‘yan Kannywood

A jerin sunayen tawagar yakin neman zaben Bola Ahmed Tinubu da Kashim Shettima, an samu jerin jaruman Kannywood da suka samu shiga.

Daga cikinsu akwai mawaka, ‘yan fim din maza da mata da suka hada da Maryam Yahaya, Mansura Isah, ‘Dan Musa da sauransu.

Tinubu ya Gwangwaje ‘yan fim da kyautar miliyan 50

A kwanakin baya da Bola Ahmed Tinubu ya ziyarci jihar Kano, ya baiwa masana’antar kyautar kudi har Naira miliyan hamsin bayan ganawa da yayi da jaruman tare da masu ruwa da tsaki.

Asali: Legit.ng

Online view pixel